TAMBAYA TA 63


*HADISIN FALALAR GOMAN FARKO NA ZUL-HIJJA BAI INGANTA BA*

*Tambaya*

AssalaamuAalaikum, Dr barka da safiya, Don Allah menene ingancin wannan hadisin Falalar Goman Farko Na Zul-Hajji....An karbo Hadisi Daga ibn Abbas (R.A) ya ce Annabi (SAW) ya ce:Ranar daya ga watan zilhijja ita ce ranar da Allah, (swt) ya gafartawa Annabi Adam (A.S). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah(SWT) zai gafarta masa kowane irin zunubi tsakaninsa da shi, (2) Ranar biyu ga Zulhijja ita ce ranar da Allah
(SWT) ya karbi Addu’ar Annabi Yunus (A.S) ya fitar da shi daga cikin kifin da ya hadiye shi, Wanda ya azimci wannan rana yana da lada
kwatankwacin wanda ya raya shekara da ibada, (3) Ranar uku ga Zulhijja ita ce ranar da Allah, (SWT) ya karbi addu’ar Annabi Zakariyya (A.S), ya ba shi haihuwa. Duk wanda ya azimci wannan
rana Allah (SWT) zai karbi adduo’insa, (4) Ranar hudu ga Zulhijja ita ce ranar da aka haifi, Annabi Isah (A.S). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah zai kare shi daga talauci da musibu.(5) Ranar biyar ga Zulhijja ita ce ranar da aka haifi Annabi Musa (A.S). Duk Wanda ya azimci wannan rana Allah (SWT) zai kare shi daga
munafunci ko azabar kabari, (6) Ranar shida ga Zilhijja ita ce ranar da Allah (SWT) ya yi budin alkhairi ga Annabi (SAW). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah zai dube shi da rahama, kuma ba zai azabtar da shi ba. (7) Ranar bakwai ga Zulhijja ita ce ranar da Allah
(SWT) zai sa a rufe kofofin wuta, ba za a bude su ba har sai adannan kwanaki goma sun wuce.Duk wanda ya azimci wannan rana Allah zai rufe, masa kofofi talatin na tsanani a rayuwarsa a buda masa kofofi talatin na sauki, (8) Ranar takwas ga Zilhijja ita ce ranar da ake
cewa, ranar tarayya.Duk wanda ya azimci, wannan ranar, babu wanda ya san adadinsa sai Allah, (9) Ranar tara ga watan Zulhijja ita ce ranar hawan Arfa. Allah yana gafartawa duk Alhazan da ke wurin Arfa. Wanda kuma ba ya wurin aikin Hajji, idan ya azimci wannan ranar, Allah yana gafarta masa zunibinsa na shekarar da ta gabata,
da kuma shekarar da ke tafe.(10). Ranar goma ga Zulhijja ita ce ranar layya.Duk wanda Allah ya horewa abin da zai yi layya, idan ya yanka dabbarsa, digon jini na farko da zai fara diga a kasa zai zama gafara gare shi da iyalinsa.
 

*Amsa*
Wa'alaikumsalam,

To dan'uwa wannan hadisin ba shi da asali, duk da cewa ya shahara a balackberry, don haka ya wajaba a daina yada shi, a kuma tsawatar da mutane game da karantar da shi, tunda bai tabbata daga bakin annabi s.a.w. ba, wasu malaman ma sun ce hadisin karya ne.

Don neman karin bayani duba fataawaa Allajana Adda'ima mai lamba ta:20803.

Amma akwai wasu hadisan da suka tabbata akan falalar goman farko na Zulhijja, wadanda sun wadatar daga barin wanda ka ambata.

Allah ne mafi sani 

*Dr, Jamilu Zarewa*

1st Zulhijja 1436 .

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*
______________________
Ku kasance damu a

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)