Assalamu Alaikum.
Tambaya
Mace me jinin haila sai hailar ta zarce mata har ta zama Istihala to ya za ayi ta gane haila ta dawo mata?
.
Amsa:
—Idan ya kasance tana da sananniyar al'ada kafin jinin rashin lafiyar ya same ta; misali a ce tana yin kwana biyar ko shida, to ita za ta zauna gwargwadon kwanakin al'adarta, idan kwanakin sun kare sai ta yi wanka ta ci gaba da ibadunta, ta dauki jinin da ya ci gaba da zuwa a matsayin jinin rashin Lafiya.
—Idan ba ta da al'ada sananniya amma kuma za ta iya bambance jinin nata: to a wannan halin sai ta dauki jini mai siffar jinin haila a matsayin hailarta, sauran jinin kuma da ba shi da siffar na haila sai ta dauke shi a matsayin jinin rashin Lafiya.
—Idan ba ta da al'ada sananniya, kuma babu wata siffa da za ta bambance tsakanin jinin haila da ba na haila ba, to a nan sai ta zauna iya kwanakin da galibin haila yake kasancewa, wato kwana shida ko bakwai a cikin kowane wata; domin wannan ita ce galibin al'adar mata. Allah Ya sa mudace.
Wallahu A'alamu.
Don neman Karin bayani sai a duba
تنبيهات على Ø£Øكام تختص بالمؤمنات.
na babban malami Sheikh Saleh bn Fauzan Al-Fauzan.
.
*05/11/2018.*
Daga Zauren
*🕌Irshadul Ummah WhatsApp.*
Ku turo da cikakken suna da address zuwa wannan number 08166650256 don shiga group dinmu a WhatsApp.