TAMBAYA TA 71


Tambaya
:
Shin wai wajibi ne Mace ta yiwa Mijinta hidimar gida kamar irin su girki da sauransu ko kuma ihsani ne kawai a kanta in ta ga dama tayi ko ta ki yi?
:
Amsa:
:
Ko shakka babu wannan tambaya ce mai matukar muhimmanci, danhaka Malamai sunyi sabani dangane da cewa shin wajibi ne Mace ta yiwa Mijinta Hidimar gida kamar girka abinci da sauransu, ko ba wajibi ba ne? Mafi yawa daga cikin Malaman da ke Mazhabobin Shafi'iyya, Malikiyya, da kuma Hanabila. Suna ganin cewa ba wajibi ba ne a kan mace ta yiwa mijinta hidimar cikin gida, to amma wasu daga cikin Malamai kamar Mazhabin Hanafiyya sun tafi ne a kan cewa wajibi ne Mace ta yiwa Mijinta hidimar cikin gida.

Hujjarsu a nan kuwa itace, sukace Manzon Allah(ﷺ) Ya raba ayyuka tsakanin Sayyadi Aliyyu da kuma Matarsa Fatima lokacin da ita Fatima taje gida tana so a taimaka mata da baiwa wadda za ta rika tayata ayyuka domin hannunta har yayi kanta saboda aikin gida, daga nan sai Manzon Allah(ﷺ) ya rabawa kowa aikin da zai ke yi, sai ya dorawa 'Yarsa Fatima nauyin kula da ayyukan da suka shafi cikin gida, shi kuma Aliyyu a ka dora masa nauyin kula da ayyukan da suka shafi waje.
:
Wani sashe daga cikin Malaman Mazhabin Malikiyya sun kafa hujja da wannan Qissa (ta Aliyu da Fatima) cewa wajibi ne a kan Mace ta yiwa Mijinta hidimar da ta shafi cikin gida a bisa ga al'ada irin ta su, kamar irin su: shara, wanke-wanke, girki, gyara shimfida, wankan yara, da dai sauransu:

Shi kuma Miji wajibi ne a kansa yayi ayyukan da suka shafi wajen gida a bisa ga yadda al'adun su ya ke, kamar irin su: Kawo kayan kwalliya, kawo cefane, nemo abinda za a ci, dinka musu tufafi, da dai sauransu. Wato shi Miji ana so ya zama shi ne ya ke rike da matsayin Ministan harkokin wajen gida, ita kuma matar ta zama Ministar harkokin cikin gida.
:
Wannan ta sa da yawa daga cikin Malamai sukace wajibi ne mace ta yiwa Mijinta hidima gwargwadon irin yanayin yadda al'adarsu ta ke, domin al'adar Mutane ta kan sha bam-bam daga wani garin zuwa wani garin, sannan yanayin irin nau'in ayyukan su ma su kan sha bam-bam, domin irin hidimar da Mace 'yar birni za ta yi wa Mijinta, ta sha bam-bam da irin hidimar da Mace 'yar kauye za ta yiwa Mijinta, hakanan abinda Mace mai karfi za ta iya yi ba zai zama iri daya da na Mace me rauni ba. Danhaka kenan hukuncin yana tabbatuwa ne gwargwadon al'adun kowanne bangare da kuma yanayin zaman takewarsu.
:
Danhaka dai maganar da tafi inganci cikin sabanin da Malamai sukayi kuma take da dalilah' masu karfi, itace cewa wajibi ne mace ta yiwa mijinta hidimar gida, domin lokacin da Fatima tazo ta na neman a taimaka mata da bawa, Manzon Allah(ﷺ) bai ce da ita ba aike ba wajibi ba ne a kanki kiyi masa hidima ba, karshe ma dai ya kara tabbatar da ita ne a kan cigaba da yi masa hidima.

 Kuma ace mace mai matsayi kamar Fatima 'yar Manzon Allah(ﷺ) kuma shugabar Matan Aljanna gashi ance sai ta yiwa mijinta hidima amma wai wata ta ke ganin cewa ai ba dole ba ne wai girki ma sai taga dama za ta yi? Lallai, to wacce Mata ce ta ke da matsayin Fatima a cikin Mata?
:
Sannan Malamai sukace Allah(ﷻ) yace:

الرجال قوامون على النساء
MA'ANA:
Maza su ne masu karfin iko a kan Mata.
:
To idan a kace wai Mace ba za ta yiwa Mijinta hidima ba to fa kenan ya zama wajibi sai dai shi Mijin ya ke yin komai da kansa kenan ita kuma ta na kwance ta na kallonsa, idan kuwa har haka ta kasance kenan ya zama Matar itace ta ke iko a kan Mijin ba wai shi Mijin ba ne ya ke da karfin iko a kanta ba. Sannan kuma da wanne mijin zai ji? Da hidimar cikin gidan zaiji ko kuma da fita neman abinci?

Danhaka dai Mata sai dai kuyi hakuri wajibi ne ku yiwa mazajen ku hidimar cikin gida:

※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Post a Comment (0)