TAMBAYA TA 74


*AZUMI GOMA A FARKON ZUL-HIJJA ?*

*Tambaya:*

Assalam alaikum Dan Allah mlm menene ingancin azumi Guda goma da ake awatan zulhijja?

*Amsa:*

Wa alaikum assalam, Hadisi ya tabbata a Sunan Annasa'i: Annabi (s.a.w) ya kasan ce yana azumtar kwanaki Tara na farkon Zul-hijja.                              
Ba'a azumtar rana ta goma saboda ita ce ranar sallah, Annabi (s.a.w) ya haramta azumtar ranar sallah a hadisin da babban sahabi Umar ya rawaito.                             
Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
3/8/2016.

Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
Post a Comment (0)