YADDA AKE KWALLIYA A LOKACIN ZAFI


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Yadda Ake Kwalliya A Lokacin Zafi_*

Ko kun san cewa kwalliya da ababen maiko bai dace ba a wannan lokacin? A wannan lokaci ne fitowar kuraje kamar su pimples da blackheads babu wahala a sakamakon irin maikon da fuska ke tarawa.

Idan ana son kulawa da kurajen fuska da kuma hana wasu fitowa, ga wasu shawarwari da ya kamata a bi:

* Hoda; Idan za a yi amfani da hoda a tabbata cewa hodar ba ta da maiko. A yi amfani da hodar da za ta tsotse gumin fuska. Kuma ana amfani da kala mara duhu domin ta haskaka fuska.

* Ana amfani da prima kafin a dora hoda a fuska. Shi prima yana hana kwalliya bacewa da wuri, wato yana dan rike kwalliya.

* Kamar yadda a wannan lokacin ba za a so sanya bakaken kaya ba ko kuma kaloli masu duhu, haka fuskar ma ba komai za a shafa mata ba, sai a samar mata kala mai haske. Kada kuma a manta shafa hoda mai haske a kan hanci.

* A rage amfani da janbaki mai maiko domin zafin rana na sanya shi narkewa kuma hakan na bata kwalliya sosai.

* Kada a manta idan za a yi amfani da gazal ko kayan kwalliyar fuska, kamar su mascara da sauransu a yi amfani da wadanda idan ruwa ya taba ba zai bata kwalliya ba.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)