TAMBAYA TA 76


*_NI CE NA FARA AZUMIN DHUL HIJJA SAI JINI YA ZOMIN YAYA NIYYATA TA KE ?_*

Tambaya

Assalamu alaikum malam nice nafara azumin zul hajji sai jini yazomin yaya niyyata take Allah yakarawa malam hasken makaranta

Amsa

Idan jinin al'ada ya zo wa mace alhali tana azumi, za ta dakatar da azumin, kasancewar jinin al'ada na hana d'aukar azumi, kamar yadda yake lalata azumi idan ana cikin yinsa.

Idan mace ta yi al'ada a cikin azumin da a ke yinsa a jere da niyya guda d'aya kamar azumin Ramadan (bisa ra'ayin malamai mafi k'arfi), idan jinin ya d'auke, za ta jaddada niyya sannan ta cigaba da azuminta. Amma idan kuwa azumin da ba dole ne a jeranta shi ba, wanda hakan ke sa a yi niyyar azumin kowace rana (kamar azumin goman farko na watan Dhul Hijjah), macen da jinin al'ada ya zo mata bayan ta fara azumin, za ta dakata. Idan jinin ya d'auke, sai ta yi niyya ta cigaba da azuminta tunda dama ana yin niyyar irin wannan azumi ne a kowane dare.

Wallahu A'alam.

Amsawa
Sheikh Dr. Ahmad Bello Dogarawa

5 Dhul Hijjah, 1439H
16 August, 2018

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*
______________________
Ku kasance damu a

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)