TSUMIN BITA ZAI-ZAI

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Yadda Ake Hadin Tsimin Bita Zai-Zai_*

Wannan hadin tsimin shi ake cewa tsimin bita zai-zai. Wannan tsimin ana
yinsa ne don gamsar da maigida da nishadantar dashi, idan mace tayishi mijinta ba zai taba jin yana sha'awan wata ya mace a wajen in ba ita ba. Kuma yana sanya ni’ima da
danshi da lema, abin sai wadda ta gwada. 

Wacce take so ta
hada wannan tsimi, sai ta nemi wadannan abubuwa kamar haka:
1- ciyawar bita zai-zai.
2- Aya.
3- Garin Masoro
4- Garin Citta.
5- Kumbura sha’awa.
6- Garin Kanunfari
*Bayani;* Zaki sami ayanki manya sai ki jika ayan da dare kafin gari yawaye ta jiku, sai ki wanke sai ki kai a markada tare da ciyawar bita zai-zai da kumbura sha'awa, idan ki markado sai ki dan dora akan wuta ki dauko garin citta da garin kanunfari da na mosoro sai ki zuba a cikin ruwan ayan nan sai ki bar shi akan wuta na kamar minti biyar, sai ki sauke, kar ki bar shi ya sha wuta da yawa, bayan ya huce sai ki tace sai ki sa kankara ko ki sa a cikin firiji, ana sha, don yana lalacewa in ya dade. Da yardan Allah za a bada bayani.


Wabillahi Taufiq.


Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*

Post a Comment (0)