"TUNATARWA CE"
nasihar .
```ILLOLIN SOYAYYA DA DALIBA KUMA SOYAYYAR DA BA AURENTA MALAMI ZAIYI BA....15/06/2020
Atakaice daga cikin illolin soyayya tsakanin daliba da malamin makarantar ISLAMIYA ke haifarwa gasu kamar haka:
1-Tana Haifar da Rashin Adalcin Malami.
2-Tana Haifar da Raini a Idon Kawayen wadda malamin yake So.
3-Tana Rage Yin Aikin koyarwa bisa Ikhlasi mai Kyau.
4-Idan akai Rashin Sa'a Aka samu Sabani Tana Haddasa gaba Tsakanin malami da Daliba. Kaga malami Har jira yake dalibar tayi Laifi.
5-Tana bada dama Ga Dalibai suma suyi da, Ansamu matsala suma suce malam wane da wane ma sunayi.
6-Tana bata Sunan Makaranta dayima malamai Kudin Goro ace kowa nayi.
Idan ka kasance Malami mai koyarda taron yan'mata budare da harma da zawarawa, sai Kayi taka tsan-tsan wallaahi Sosai, don duk rudani sai ka shigeshi, shiyasa tun farko ya kamata ka kasance kanada Ka'idoji da sharudda, duk Wadda bata cikaba to lallai ka tsawatar in taki ka koreta shine alkhairi, na daga cikin sharuddan da yakamata kasanya sunhada da:
1- Hanasu Kwalliya lokacin zuwa Islamiyya.
2- Hanasu sanya Matsatsun Kaya lokacin zuwa Islamiyya.
3- Hanasu sanya koda Jan baki ne, Idan bushewar baki suke tsoro to su Shafa FARIN MAI KO VASELINE a bakinsu.
4- Hanasu Lalle musamman Dise ko kuma su sanya safar hannu lokacinda tayi Dise. (safar kafa kam yakamata tazamto wajibi a makarantarka).
5- Cikakken Tufafi na Musulunci bakuma Kaya mai Shara Shara ba.
6- Hanasu sanya turare, ko wani Abu mai Kamshi .
7- Su Girmama Muryarsu yazama kamar na maza lokacinda take Karatu, in kanajin harda, ko Karin Karatu (ka hanasu kashe murya a kowane yanayi
8- KADA KA KEƁE DA ƊAYA DAGA CIKIN ƊALIBA DON KARA KARATU Ko WATA MAGANA TA DABAN.( aikata hakan yakan jawo zargi daga sauran dalibai kuma zata iya zuwa ta fadima iyayenta ko yan'uwanta wata maganar da bakayi ba kuma babu mai iya fiddaka sai Allah S.W.A Kawai)
9.Kayi kokarin hana dalibbai mata kiranka ga waya ko yin chart dasu a social media.
10- Kadaina yawan sake fuska da dariya garesu. (Ka Kama kanka sosai da Mutuncinka)
11- Nuna musu equality (matsayinsu guda ne a wajenka ) kada kanuna fifiko ko Kadan...
Tabbas idan mukabi wannan takaitacciyar tunatarwai hakika zata amfanemu da duk sauran malaman Islamiyu gaba daya
Allah ta'ala yakara bamu ikhasi wajen koyarwa kuma ya bamu lada yayi mamu sakamako da aljanna Firdausi. Allah ta'ala ya ba malamanmu na Islamiyya kariya a kowane yanayi. Allah kuma ya qara bamu fahimtar juna tsakaninmu da iyayen daliban mu domin qara samun damar tarbiyyantar da dalibai akan tafarkin sunna.
'Dan uwanku amusulunci
Muhammad Zayyanu ya'aqub {ABIY ABDIRAHMAAN}