WANNAN ABUN DUBAWA NE
Bissmillahir Rahmanir Raheem.
Assalamu Alaikum Warahamatullah Wabarakatuhu.
Haihuwa abin farinciki ne da duk gidan da aka same ta a ciki za ka iske shi cike da farinciki da murna. Wannan ya sa mutane daga ko'ina kan ziyarci gidan domin taya su murna ko kuma su kira a waya su yi musu fatan alheri. Abu mafi girma da aka fi aikatawa a irin wannan hali dai shi ne yi wa abinda aka haifa addu'a. Za ka ji mutane na cewa: 'Allah ya raya shi' da makamantansu. Kaɗan ne daga ciki su ke tsayawa su yi wa wannan yaro ko yarinya addu'a da ta dace. Haƙiƙa babu wanda zai so ace an yi haihuwa a gidansa ko gidan wani nasa kuma a ce wannan ɗa ko 'ya ta koma zuwa ga Allah, to amma fa, babu wanda kuma zai so ace wannan ɗa ya girma ya zama ɗan banza.
Don haka, me zai hana ka karantawa wannan jinjiri abinda ya sauƙaƙa gare ka dangane da alƙur'ani? Me zai hana ka roƙa masa tsari daga shaye-shaye, sata kisan kai da sauran bala'o'i na zamani? Me zai hana ka roƙa masa abubuwan alheri irin su samun damar haddace alƙur'ani mai girma, zama mai hidima ga Addinin Musulunci, zama mai biyayya ga iyaye da sauran abubuwa makamantansu?
Shin ba ku tsammanin cewa jajircewa wajen aikata haka ka iya taimakawa wajen samun nagartattun yara da za su taso su zama nagartattun mutane da za su amfani al'umma nan gaba? Amma in har addu'ar mu ta zama kawai akan Allah ya raya su ne kawai ba wai ya shiryar da su ba ko? To irin su ne sai su girma su gallabi al'umma kuma su ƙi mutuwa da wuri, a yi ta fama da su. Sannan ya kamata mu sani cewa da ka haifi ɗa fa ya girma ya zama ɗan banza gara ace ya mutu tun yana ƙarami ko kuma ma bai zo duniyar ba, ya fi maka alheri.
Muna fata Allah ya sa duk wata mace musulma da ke ɗauke da juna biyu Allah ya sauke ta lafiya, Allah ya ba su ikon yi wa abin da aka haifi tarbiyyar da ta dace kuma ya wadata su da abin yin tarbiyyar. Allah ya sa abinda aka haifan ya zama nagari, hafizi, haziƙi, mai jin tsoron Allah kuma mai tausayin iyayensa da sauran Al'ummah. Allah ya shiryar da mu da zuri'armu kuma ya yafe mana laifukanmu.
Subhanak Allahumma Wabi Hamdika Ash Hadu Anla Ila Ha Illah Anta Astagfiruka Wa Atubu Ilaika.
Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu.
©️✍🏻
Jamilu Abdurrahman
+2348185819176
19th June 2020