WASU DAGA HANYOYIN MALLAKE MIJI


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Wasu Daga Hanyoyin Mallake Miji_*

1- ki zama mai tsaftar jikinki, gidanki, abincinki, da sauransu.

2 - Ki dinga girmama Iyayan mijinki da ‘yan uwansa da abokansa.

3 - Kada ki zama mai satar kayan mijinki.

4 - Kada ki zama mai satar fita unguwa.

5 - Ki guji Leke a gidan mijinki, dan yana daga cikin abinda yake raba Aure a tsakanin Hausawa.

6 - Ki dinga godewa mijinki a cikin abinda ya baki.

7 - ki kiyaye abinda mijinki ya fi so.

8 - ki kiyaye abinda mijinki ya fi sonci da safe, rana, dakuma dare.

9 - Ki dinga yabawa mijinki kwalliyarsa.

10 - Ki dinga yawan neman shawarar mijinki akan duk wani al’amari da zaki yi.

11 - Ki yi kwalliya ki tsane tsaf kafin dawowar mijinki.

12 - Ki dinga sanya turaren wuta a dakinki, kuma ki kasance mai sanya turare a jikinki a duk lokacin kwanciya.

13 - Lallai ki yi kokarin gama aikace-aikacenki kafin dawowar mijinki.

14 - Kada ki bari mijinki ya dawo ya sameki gaja-gaja, ki sani kazanta tana haifar da kiyayya.

15 - Ki zama mai yawan canza zanen kunshin kafarki da kuma zanen kitso.

16 - Kada ki ce mijinki sai ya saya miki abinda ba shida ikon saye.

17 - Lallai ki yi amfani da ilimi wajen yanke dukkan wani hukunci.

18 - Ki yi shiru a duk lokacin da mijinki yake yi miki fada ko Nasiha.

19 - Kada ki zama Al-mubazzara mara tattali.

20 - Kada ki tara kayan wanki da yawa a daki, naki ko na mijinki suna wari.

21 - Ki tanadi kayan kwalliyar gida bayan na zuwa unguwa.

22 - Ki kula da yanayin da zai nuna miki cewa mijinki yana cikin Nishadi ko Damuwa.

23 - Kada ki ringa baiwa kawayanki labarin sirrin dake tsakaninki da mijinki.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)