ABUBUWAN DA MATA KE BUƘATA A WAJEN MAZAJENSU

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI* 

*_Abubuwan Da Mataye Suke Bukata Ga Mazajensu_*

*_1.TSARI:_* Duk wata ‘ya mace tana son ta ga mijinta mai tsari, ba wai tsari irin na magana ba. Abin da nake nufi da haka shi ne, miji ya kasance yana da tsarin rayuwa mai kyau, ba mutum ya zama shashasha maras kan gado ba.

*_2. KYAU DA KWALLIYA:_* Wasu matan suna son mutum mai kyau da kwalliya ba irin su wancan nanka ba, sau da yawa za ka ga mata suna sonsa saboda tsabar kyau da Allah ya ba shi, da kuma iya kwalliya kamar ɗawisu.

*_3. KALAMAI:_* Yana da kyau miji ya zama ya iya kalaman da za su janyo hankalin matanshi, rashin iya kalami kan janyo rashin so. Maimakon haka sai ka zama tamkar ɗan bora a wajenta. Dole ne ka kasance ka iya kalaman da zaka birge matanka.

*_4. KIRKI DA KULAWA:_* Miji yakan tafiyar da zuciyar ya matarsa dalilin kasancewa mai kulawa da kirki. Misali duk bayan wani lokaci sai dunga tambaya meki ke so ko mezan samo ki.

*_5. KAR KA RIƘA YAWAN YI MATA MAGANA GABAN YAYA:_* Ka guji yawan yin mata magana na zafi a gaban yayanta ko fada agaban yayanta yana rage so da kauna a tsakani ma'aurata. 

*_6. BARKWANCI:_* Idan ka kasance mai raha ga matarka to nan da nan za ka sace zuciyarta. Misali ka rika ce mata a duk lokacin da kake tare da ita, tauraruwan zuciyata, ɗaya tamkar da goma cikin sahun mataye, a do da kyau siffarki ce, murmushinki ke sanya zukata fara’a. gimbiya adon ‘yan mata. Da sauran su. Kana mai ambaton haka cikin murmushi da shauki irin na soyaya kuma dole ne hirarku ta kasance mai amfani ba ka yi ta zuba ba, har sai ka gundure ta. Yawan magana ba shi da tasiri a zamantakewa muddin ba magana ne masu ɗauke hankali da san ji ko rashin gundura ba.

*_8. KYAUTATAWA:_* Sai dai kuma duk da na yi bayani kan cewa kwaɗayi bashi da kyau a ma'aurata, hakan ba shi yake nuna ba za ka kyautatawa matarka ba. Hasali ma idan kai haka, to za ka ƙkara ƙkarfin shakuwa ne tsakanin ku da juna. Sai dai idan za a yi kyauta a duba me mata take da bukata a daidai wannan lokaci. Misali, kar ka kawo mata hoda a lokacin da take bukatar turare, atamfa, yayin da ita kuma leshi take so.

Wabillahi Taufiq.


Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*

Post a Comment (0)