YADDA AKE KUNUN GYAƊA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Yadda Ake Kunun Gyada_*

Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
* Danyar gyada
* Dafaffiyar shinkafa
* Sugar
* Madara
* Leman tsami
* Filawa
*Bayani;*
1- Da farko zaki gyara gyadarki, ki wanke ta, ki shanyata ta bushe sai ki soyata sama sama ki murje ta bawan ya fita, sai a kai markade, idan an markado miki ki tace da abin tata ko rariya,sai ki zuba a tukunya ki dura a wuta ki dakko dafaffiyar shinkafarki ki zuba a ciki kina juyawa har ya tafasa(yayin da kika dura kullin a wuta baza ki tashi ba saboda kar ya tafaso ya zuba, sai kina zaune a gurin kina juyawa) sai ki dakko filawarki ki damata da ruwa ya danyi kauri.

2- Idan ya tafasa sai ki zuba damammiyar filawarki a ciki a hankali kina juyawa har kaurinsa yayi miki yadda kikeso sai ki sauke ki matsa leman tsami a ciki ki juya.

3- Ki barshi ya huce sai kisa sugar da madara asha (shi sugar din sai kunun ya huce ake zubawa saboda in kika zuba sugar da zafi shine yake sa kunun ya tsinke).


Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*

Post a Comment (0)