_*======BUDURCI NA=====*_
*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*
Fitowa ta daya=*{17}*
Akwai dalilai da dama da ba lalle ba ne mace ta yi jini a kwanciyarta ta farko da namiji,
kamar yadda Dakta Sonia Naik, kwararriyar likitar mata da ke zaune a Delhi ta sheda wa BBC.
Likitar ta ce: ''Idan mace ta yi wasan motsa jiki sosai ko ta rika wasa da farjinta, domin jin dadi ta hanyar tura dan yatsa ko wani abu a ciki domin sha'awa, to bai zama lalle ta yi jini a lokacin saduwarta ta farko da namiji ba.
Haka kuma idan namijin da zai sadu da ita ya yi mata a hankali,
musamman har su yi amfani da mai ko wani abu da zai saukaka shigarsa cikinta,
to wannan ma na iya hana ta jini a saduwar ta farko.
To amma ita Anita a halin da ta samu kanta a ciki ta san cewa wannan gwaji na budurcin shirme ne kawai,
domin ta riga ta sadu da mijin nata tun kafin su yi aure. Amma ta ce ita kam ba ta shirya ma abin da zai biyo baya ba na cin mutuncinta, idan aka gano cewa ai ta riga ta san namiji tun a waje.
Ta ce: ''Na dauka mijina zai kare ni a gaban wadannan 'yan majalisar magabata na garin namu,
Amma da suka tambaye shi,
ina da tsarki ko ba ni da tsarki, wato ni cikakkiyar budurwa ce ko kuma a'a' sai ya nuna wannan zanin gado wanda ba alamar jini a jikinsa, kuma ya kira ni bogi.''
Muhadu agaba insha Allah,
*GABATARWA Miftahul ilmi*
*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi
Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248