_*======BUDURCI NA=====*_
*🌻ABIN ALFAHRINA🌻*
Fitowa ta daya=*{18}*
Ta kara da cewa: ''Abin ya ba ni mamaki Shine, saboda shi mijin nawa ya rika tilasta min kwanciya da shi har tsawon wata shida.
A nan take 'yan majalisar kauyen namu suka ayyana ni a matsayin maras tsarki,
suka tafi suka ba ni wuri,
aka bar ni ni kadai a nan ina ta kuka.''
An tilasta wa mijin Anita yin auren, wanda da farko ya so ya fasa saboda ta fadi a wannan gwajin na budurci,
bayan da wasu ma'aikatan kula da jin dadin jama'a sun ji abin da ya faru, suka kai maganar gaban 'yan sanda.
Sai dai ta ce mijin nata ya zamar mata wani dodo, kan yadda yake gana mata akuba,
inda yake dukanta kullum da kuma muzanta ta.
Bugu da kari,
abin takaicin shi ne majalisar magabatan garin ta haramta wa duk ma'auratan da amaryar ta fadi wannan jarrabawa ta budurci halartar duk wani taro ko biki na garin.
''Abu dai ba sassauci har lokacin da na samu juna biyu. Mijina ya takura min da tambaya :
'Dan wane ne wannan?'
Su ma dattawan garin haka suke tambayarsa.''
In ji Anita.
Wata biyu da ya wuce mijinta ya kore ta da ita da jaririnta sabuwar haihuwa, saboda haka a yanzu tana zaune ne a gidan iyayenta. Amma ta ce kyamar da ta biyo bayan wannan gwaji na budurci da ta fadi ta shafi gidansu gaba daya,
domin hatta kannenta sun rasa mazajen aure.
Muhadu agaba insha Allah,
*GABATARWA Miftahul ilmi*
*_Ga masu sha'awar bin shirye shiryrnmu ta Telegram se yabi ta_*👇🏽
https://t.me/miftahul_ilmi
Dan kasancewa damu ta
WhatsApp
_*Miftahul ilmi*_
Se a turo cikakken suna da Address ta wan nan Number👇🏽
07036073248