FASSARAR WAƘAR MAR JAAYEN


FASSARAR WAƘAR MAR JAAYEN 


Waƙa: Mar Jaayen

Fim: Loveshhuda

Harshe: Hausa  

Shekara: 2015 

Sauti: Mithoon

Rubutawa: Sayeed Quadri

Kamfani: Tips Music

Rerawa: Atif Aslam

 Fassarawa: Jamilu Abdurrahman 

• Har Lamha Dekhne Ko, Tujhe Intezaar Karna

A kowane lokaci, jira na ke yi ko zan ga giftawarki. 

• Tujhe Yaad Karke Aksar, Raaton Main Roz Jagna

Na kasance a farke tsawon dare ina tunanin ki. 

• Badla Hua Hai Kuch Toh, Dil In Dinon Yeh Apna

Zuciyata ta samu canji a kwanakinnan. 

• Kaash Woh Pal Paida Hi Na Ho, Jis Pal Mein Nazar Tu Na Aaye (x2)

Kada (Allah ya kawo) lokacin da ba zan ganki ba. 

• Gar Kahin Aisa Pal Ho, Toh Iss Pal Mein Mar Jaayen

In kuwa irin wannan lokaci ya zo, to zan so in mutu a wannan lokacin. 

• Mar Jaayen, Mar Jaayen, Mar Jaayen, Ho Mar Jaayen (x2)

Ina so in mutu, ina so in mutu (a wannan lokacin) na ke so in mutu. 

• Tuhjse Juda Hone Ka Tasavvur, Ek Gunaah Sa Lagta Hai

Tunanin rabuwa da ke ma jinsa na ke yi kamar ta'addanci ne. 

• Jab Aata Hai Bheed Mein Aksar, Mujhko Tanha Karta Hai

A duk sanda irin wannan tunanin ya zo min, na kan ji ni a cikin kaɗaici ko da a taron jama'a ne. 

• Khwaab Mein Bhi Jo Dekhle Yeh, Raat Ki Neendein Ud Jaayen

Ko ganin hakan na yi a mafarkina take bacci ke ƙaurace min. 

• Mar Jaayen, Mar Jaayen, Mar Jaayen, Ho Mar Jaayen 

Ina so in mutu, ina so in mutu (a wannan lokacin) na ke so in mutu. 

• Aksar Mere Har Ek Pal Mein, Kyun Sawaal Sa Rehta Hai

Me ya sa na ke jin wannan tambayar koyaushe a zuciyata? 

• Tujhse Mera Taaluk Hai Yeh, Kaisa Aakhir Kaisa Rishta Hai

Wace irin shaƙuwa ce a tsakaninmu? Wace irin alaƙa ce wannan? 

• Tujhko Na Jis Din Hum Dekhe, Woh Din Kyun Guzar Hi Na Paaye

Yinin duk da ban ganki ba, me ya sa bai taɓa wucewa? 

• Mar Jaayen, Mar Jaayen, Mar Jaayen, Ho Mar Jaayen (x3)

Ina so in mutu, ina so in mutu (a wannan lokacin) na ke so in mutu. 


ƘARIN HASKE: Shin ka taɓa son wani mutum har aka kai matakin da kana ko kina jin tsoron rabuwa ko rashin ganin juna? Fasihi Atif Aslam ya zayyano mana irin halin da masoyi kan shiga a irin wannan yanayi a cikin wannan waƙa. Nagode

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
   (Mr. Writer) 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Post a Comment (0)