*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*
```// 11```
.
KARATU
Duk wani mai son cin nasara a rayuwa dole ne ya yi karatu, kodai ya yi na takarda da biro ko kuma ya yi na rayuwa, wanda duk ka ji ya ce "Ba dole sai mutum ya yi karatun boko zai zama wani abu ba" maganarsa haka take, amma wani karatu ne ya zarce zaman duniya? Ai ita duniya gaba dayanta makaranta ce, jami'a ce da take da sassa daban-daban, duk sashin da mutum yake son ya shiga zai samu, da za ka dauki mutane guda biyu; wani ya bi layin boko, wato furamare har zuwa jami'a a qarshe ya sami abin kansa, za ka taras wani ya fara da qaramar sana'a ne, ya bari ya koma wata, ko kuma ya qawata ta, za ka ji ya sha wahala iri kaza kafin ya isa wuri kaza, duk wadannan da kake gani karatu ne bambancin hanya ne kawai.
.
Mu a zamanance muna daukar wanda ake ganin kamar ya dan fi sauqi ne, wato shiga a ji, shi din ma ana qoqarin goge qwaqwalwar yaro ne tun yaranta yadda zai iya hararo abubuwan da za su amfane shi a rayuwa, babban dalilin da ya sa aka qirqiro darussan dake buqatar tunani kenan a azuzuwan yara qanana, akan koyar da yaro a ba shi aiki don ya wasa qwaqwalwarsa wajen nemo irin amsar da ake buqata a rayuwa.
.
Idan za a tura yaro wurin sana'a shi ma karatu zai yi, sai dai wannan ya fi karkata ne ga aiki, wato karatu ne amma a aikace, zai san kayan aikin gaba daya da yadda ake sarrafa su, muna da injiniyoyi irin su kanikawa, kafintoci, maqera da magina, wadannan manya-manyan Injiniyoyi ne amma ba su san haka ba, sabanin wadanda suka je makaranta, sau da yawa za ka taras wadanda suka yi karatun boko ba su kai wadanda suka yi a aikace ba, amma da ka ce Injiniya sun san da su kake yi ba wadancan ba, sun yarda da kansu sosai koda kuwa ba abin a qasa, sai su fara bin hanyoyin da za su cimma burinsu, cikin ikon Allah sai ka ga sun sami biyan buqata a dan qaramin lokaci.
.
Wadanda suka faro ta sana'a sukan dauka cewa na abinci kawai suke nema, wato abinda za su ci da iyali, duk kuwa da cewa bakanike karar abin hawanka kawai zai ji ya ce maka kaza ya lalace, in ya hau ya ce maka sai ka canza kaza, in ya bude ya ce maka ba za ka jima ba za ka canza kaza, wannan in ba karatu ba meye? Sai dai babu tsari ne na mataki, babu wata takarda da ake la'akari da ita wace za ta ba da shedar cewa tabbas mutum ya qetare mataki na kaza don haka ya zama cikakken Injiniya, sai ya dauki kansa a kan cewa shi ba injiniyan ba ne, ko ka ce injiniya in ba an saba kiransa ne ba ba zai waiga ba, da wahala ka ga ya fadada tunaninsa a kan fannin da yake ciki har ya fara saka wa a ransa zai iya qera jirgin sama.
.
Galibin wadanda suka fara sana'a a aikace sun ta'allaqa ne da motsa jikinsu wajen koyon abinda za su riqe rayuwarsu da iyalinsu kawai, akwai qarancin tunani wurin hararo sabbin abubuwa wadanda za su bunqasa sana'ar, ko qirqiro wasu sabbin na'urori da kansu wadanda za su sauqaqe musu ita, shi ya sa nake ganin wanda ya kama sana'a kuma ya shiga makarantar ya fi kowa sanin kanta, kamar yaron da ya girma a cikin bariki ne daga bisani ya shiga soja.
.
Yanzu kai da ka fara kasuwanci a gaban babanka ko kantinsa dole ka san irin kayan da mutane suka fi so, ka san nau'in da suke buqata, da lokutan da suka fi zuwa sayayya, a daya hannun dole ka iya lissafi irin na rayuwa, wato ka riqa gamsar da su ta wurin cinikayyarsu, misali mata masu ciniki, kayan da ake sayarwa a Naira 15 sai ka bar shi 13.5 dan abinda ka rage 1.5 ne kawai, akan dan wannan ragin mace za ta iya takawa daga wuri mai nisa ta zo wurinka, to bare qaramin yaron da aka aika, sai ka sayar da guda 10 wanda ya qi rage nasa bai sayar da 4 ba, in ka duba sai ka ga ka mai da kudinka har ka sami ribar da shi bai samu ba.
.
Kawo irin kayan da mutane ke buqata kowa na yi, amma lissafin sauqaqe kaya don jawo mutane da yawa wani abu ne da yake buqatar lissafi bayan dogon tunani, galibi wadanda suka hau sana'a a sama ba su cika irin wannan lissafin ba, in aka yi rashin da ce da mai sayar da kayan gwari sai ka ga ya rube an zubar, a maimakon a sauke kudin ya qare a sake kawo wani ya qare a dauko wani nan da nan, ta kowani bangare ka bi karatu na ba da gudummuwa gwaggwaba wajen cin nasara a rayuwa.
.
Ba qoqari muke mu ce wanda bai yi karatu ba ba ya cin nasara, manufar ita ce in aka hada bangarorin guda biyu an fi samun sauqi wajen isa ga buqatun mutum na cin nasara a rayuwa, nakan ga uwaye da dama sukan sa yaransu a makaranta, kuma suna tilasta su tsayuwa a wuraren aikin hannu don su sami sana'a, wani zai gaya maka cewa tun yana sakandare shi ya dauki nauyin karatunsa, na ga wani dan bumburutu kwanannan da yake gaya min cewa yana karatu ne a jami'a, yana karanta Biochemistry, yanzu yana tara kudin makaranta ne, irin wannan da wahala ka ga ya sadaukar da karatunsa a banza, ya fi kowa sanin irin wahalar da ya sha.
👂🏻👂🏻👂🏻👂🏻👂🏻👂🏻👂🏻
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
_________________________
"Wanke hannu da ruwa Mai gudana tare da Shan ruwa akai-akai da bin dokokin Ma'aikatan lafiya na daga cikin matakan kariya daga daukar cutar corona virus kamar yadda ma'aikatan lafiya suka fada
_________________________
Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```