*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*
```// 14```
.
GAMUWAR ILIMI DA BURI
Abinda mafi yawan mutane suka sani game da ilimi ko jahilci shi ne: Mai ilimi mutum ne da ya bi tsarin karatun boko a rubuce sannan ya dan hada da turancinnan, in aka sami mutum bai bi wannan tsarin ba to jahili ne, bambancimmu da qasa mai tsarki kenan, a 'yan shekarun baya an yi wasu shahararrun malaman muslunci, sun koyar da daliban jami'un qasar alhali ba su taba wuce makarantun sakandare ba, tunda har wadanda suka bi tsarin karatun daga Furamare har gaba da digiri suna daukar karatu a wurinsu, dole sai an yi wa ma'anar jahilcin gadon bawul.
.
Iya rubutu da karatu, ko bin tsarin boko ba shi ne kadai ilimi ba, a neme ka a kan abu kuma a same ka da shi shi ne manufa, duk ilimin da mutum yake da shi na kasuwanci, in zai koyar da duniyannan gaba dayanta amma ya kasa aiki da ilimin wurin zama babban dan kasuwa haqiqa babu alamar sifantuwa da ilimin, komai daqiqancin mutum ko rashin shiga makarantar boko in ya san yadda zai juya kudi, ya yi babban shago maqare da kaya ya sami ma'aikata, wannan ya fi qarfin jahili.
.
Duk mutumin da zai shata gona, ya dibi ma'aikata ya yi lissafin kudin taki da na ma'aikata ya yi bankadediyar gona, in amfani ya zo gidansa ya gyara ya sayar ya ci riba ya sake shiri don gobe wannan ya fi qarfin a kira shi jahili, ilimi da buri a hade suke ba sa rabuwa, da yawan wadanda suke karanta ilimin injiniyanci don su zama injiniyoyi ne, haka ma wanda yake koyon kanikanci duk qoqarinsa a ce yau ya zama bakanike, ma'ana dukansu dalibai ne, wanda ya iya isa inda yake so ya ci nasara kenan a rayuwarsa, a taqaice dai babu jahili kamar wanda yake ganin ya yi ilimin amma bai san yadda zai yi aiki da shi ba.
.
Yanzu dai komai iliminka da qwaqwalwarka kana buqatar zama kusa da masu ilimi wadanda za su taimake ka kan lamura, wannan ya sa za ka ga wani kamfani babba wanda bai da alaqa da shari'a amma yana da mai ba da shawara ta fuskar doka da oda, wannan aikinsa kenan nuna wa kamfanin fuskar da zai bi don guje wa aukawa cikin wata matsala, idan wanda bai yi karatu ba yana da masu fuskantar da shi sai ya yi abin mamakin da wani mutumin da ya yi nisa a bokon bai yi ba, kawai abinda kowani irin mutum yake buqata, daga kowani irin rukuni yake kuwa, shi ne: Me yake buri, yazai isa gare shi?
.
FUSKANTAR MATSALOLI
Akwai wasu matsaloli a rayuwarmu wadanda duk yadda muka yi ba za mu iya kauce musu ba, wani sa'in ba ilimi ne kafai magani ba anan, abin kan faru ba mu san da shi ba shi, tabbas wasummu suna fama da matsaloli masu baqanta rai, masu radadi a zuciya, ka ga mutum koyaushe cikin damuwa da qunci ka rasa me yake damunsa, wani ma takan kai ga hakan ya yi tasiri a cikin al'amuransa yadda dan abu kadan sai ka ga ya dauke shi sama da yadda ake buqata, yana da kyau mu fahimci cewa wannan cuta ne dake buqatar magani.
.
Koda yake hakan kan faru ne daga wani abu da aka yi wa mutum, in ya zamo bai yin shawara da kowa sai abin ya yi ta cinsa a rai har ya kai ga wannan halin, wani kuwa tsabar zato ne cewa in har wannan abin ya tabbata to shi fa ya shiga uku, daganan ya sa abin a zuciya har ta kai shi ga aika-aika a kan sana'arsa ko lamarin rayuwarsa, a qarshe da wahala nasarar ta samu masa kamar yadda yake zato, ka dubi mata dai yadda suke daukar kishi da kishiya, sam ba sa zaton alkhairi ga kishiyar, sai su fara wasu ayuyyukai da maganganu, hakan ta kai ga amaryar daganan ita ma ta fara shirin yadda za ta fuskanci uwargidanta.
.
In ta shigo ba za ta gasgata fara'a da haba-habar da za ta gani ba sai ta dan sami lokaci ta tabbatar gaskiya ne ba shigo-shigo ba ne, dan lokacin da za ta dauka kafin ta saki jiki in ba a kai hankali nesa ba sai ka ga uwargidan ta yanke qauna, ta ce ta yi kaza da kaza amma ga abinda amaryar take yi mata, in shaidanun mutane ko ragon namiji ya shiga tsakiya shikenan lamarin ya gama ragargajewa gaba da daya, babban abinda ya jawo hakan tsoro da hukunci kan abinda baka tabbatar ba.
.
Zai yuwu a sami hakan in kana da shagon sayar da takalma ka ji wani shi ma zai yi a kusa da kai, sai ka yi tsammanin cewa kai kuma taka ta qare kenan za a koma wurinsa, daga lokacin ka rasa kasuwa kenan, ko kana da burin gina gidan buredi sai aka ce akwai kusan gidaje guda uku, ba ka duba yawan maciyan ba da yawan buqatunsa sai ka duba gidajen buredin kawai, wannan 'yar matsalar da samu in ba a yi sa'a ba shikenan komai ya tsaya qila ma daga lokacin ba wani abin da za ka yi tunanin yi an riga an gula maka kissafi, bayan ga lissafe-lissafennan barkatai.
Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```