*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*
```// 13```
.
KARKASUWAR BURI
Ba wani dan adam da ka sani wanda bai da burin da yake so ya cimmasa a rayuwa, sai dai kamar yadda muka fada ne, wani ya san abinda yake nema, wani yana zaune ne kawai bai san abinda yake buqata ba, wani ya san komai amma hanyar da za ta kai shi zuwa ga burin ne bai sani ba, wani ya san hanyar kuma yana kanta, amma matsalar ya kasa tsayar da abu guda da yake burin isa gare shi, ga komai a zagaye da shi amma bai san wanda zai fuskanta ba, qarshe sai ya zo dab da wannan ya bar shi ya koma wancan, a qarshe ya gaji da wahala ya koma hannu-rabbana.
.
Da za ka kasa burinka zuwa gida biyu da zai fi ba da ma'ana, wato a sami burin da yake dab da kai, wanda ba zai buqaci aiki mai baqar hawala ba, ba zai dauka maka lokaci ba, ba zai buqaci kudi masu yawa ba, misali kana son ka zama babban Injiniya, wanna buri ne da yake nesa da kai, matuqar baka ma shiga jami'a ba, magana ce da za ta dauki tsawon lokaci, ta buqaci kudi, da juriyar karatun, wanda yake son ya gida katafaren masana'antar lemon kwalba, kuma a yanzu dan shago ne gare shi bai da cikakken jari wannan buri ne mai tsawo wanda zai iya dauke rabin rayuwarsa kafin ya sami biyan buqata, akwai maganar tara kudi, sayen fegi da na'urorin aiki.
.
Babban abinda ya dace a rayuwa shi ne farawa da buri mafi kusa da mutum, wanda za a iya kaiwa ga nasara ba tare da an bata lokaci ba, kuma za a sami kudin da ake son a yi amfani da su ba tare da jiki ya jigata ba, akwai matakai har 3 da suka zama dole ga mai son cin nasara ya taka su kafin ya kai ga nau'in nasarar da yake buqata:-
1) Tabbatar da abu guda wanda kake son ka cin masa, da yawammu muna ganin kamar baiwa ce mutum ya sami mabambantan sana'o'i, ko kwalayen digiri na farko da dama, ba mu san cewa hakan kan hana mu mu natsu a wuri guda ba, ita kuma nasarannan hanyoyi ne da dama take da shi amma ita kadai ce, in ka ce duk hanyoyinnan sai ka bi su kafin ka isa gareta babu kokwanto za ka kai a makare.
.
Domin ka kama wannan hanyar ka yi nisa ka bar ta ka dauki wata, ka faro daga farko ita ma ka bar ta ka dauki wata, kafin ka kai ka bar ta ka sake dauko wata, wanda ya dauki hanya daya tal tuni ya manta cewa ya biyo hanyar, ka yi qoqari ka sami buri guda a zuciyarka ka saka shi a gaba, in ka cimmasa ka sake qulla wani shi ma ka yi qoqarin isa gare shi, ba za ka bar shi ba sai ka tabbatar da ka isa gare shi sannan ka dauko wani, in ba haka ba tara abubuwa da yawa kan kawo tarnaqi a lokacin da mutum yake qoqarin cin nasara a cikin al'amarinsa, sai dai zai yi kyau mu fahimta, ba cewa muka yi kuskure ne ba ka ci nasara a cikin al'amuranka, amma cewa muke ka zabi abu guda tukun, in ka same shi ka sake dauko wani.
.
Wallahi na yi zamani da wani mutum wanda ya bar karatu tun yana furamare a dalilin bai gane komai, haka yake dudum ba Arabi ba boko, duk wani rubutu in ka cire sunansa da ya ci duka a makaranta a dalilinsa ba abinda ya iya, sai dai kuma maqeri ne na wuqaqe kai har da bindiga mai aiki da harsashin soja, masucin kifi ne kuma ya iya farautar makware, tela ne shi, ban san lokacin da ya koyo gini ba, yana aikin gyaran kayan wuta ko sanya wa mutum wuta a daki, kafinta ne shi na sama da qasa, yakan dauki mashin ya zagaya express a wancan lokacin, yanzu ma mota yake hawa, yana da qwaqwalwa ta ban mamaki a duk sana'ar da yake son yi, bokon ne babu, sai dai matsalar ban san wata sana'a qwara daya da ya shahara a kai ba wace zan ce ya yi fice kuma zai iya zama wani abu nan gaba a dalilinta, ma'ana wace ya bunqasa ta a dalilin qwaqwalwar da Allah ya ba shi, har kuma mutane za su amfana da shi, matsalar kai komon kenan.
.
2) Tsarin isa ga burin, matuqar ka sami burin da kake son ka cin masa sai ka natsu ka tsara hanyoyin da za bi don ganin lallai ka isa gare shi, rashin tsari shi ne babban matsalar da mafi yawan mutane suke fama da shi, na ga wani da yake son ya yi shago a kusa da makaranta, abin takaici da wahala ka ga dalibi ko malami ya zo shagon ya sami abinda yake buqata, lokacin da muka ba shi shawarar ya fara kawo abinda muke buqata mana, sai ya ce shi ya taba irin wannan sana'ar ba ta ba shi ribar da yake buqata ba, na ce a zuciyata to ai abinda kake so ka sayar yanzu mu kuma ba mu da buqatarsa, kenan ananan dai yau kamar jiya, shi yana son ya sayar da abinda mutanen wurin ba su buqata ne, ka ga batsari anan.
.
Komai kyawun abinda kake so ka yi in babu lafiyayyen tsari aikin banza ne, kodai a gaza yi, ko a yi din ya qi qarko, in dai kana so ka ci nasara ka nemo tsarin da farko a qwaqwalwarka, in ma zai yuwu ka rubuta ko ka zana a takarda maganin mantuwa, a hankali lamarin zai fadada, ka ga sai ka janyo wasu kusa yadda ko ba kanan harkar za ta ci gaba ba za ta tsaya cak ba, za a yi tsarin ne daki-daki daga wannan sai wancan, ana bin matakan sau da qafa, in ma mutum bai yi boko ba ba zai rasa wanda za su yi tsarin tare ba, yadda in ya manta wani abin za a tuna masa, wannan shi ne matakin tsakiya.
.
3) Sai kuma matakin qarshe wato zartarwa, inda mutum zai fara bin tsarinnan amma a aikace, ya yi iya bakin qoqarinsa wurin ganin cewa yana bin tsarin ne kamar yadda ya dauko tun farko, ba tare da gaggawa ba, za mu yi maganar gaggawar nan gaba in sha Allah, wato kamar mai koyon aiki ya fara tunanin cewa yana shan wahala ba a ba shi komai, sai ya tara kudi ogansa ya kwashe duka, irin wannan kalle-kallen gaggawa ne, in mutum bai sa'a ba sai ya bar wurin kafin ya iya, saboda tunanin cewa ana cutarsa, na sha ganin wadanda suke fara aiki su bari saboda raina albashin da ake ba su, ba su da wani tunani na cewa nan gaba za su iya zama wani abu ta wannan hanyar kuma za su sami duk abinda suke so.
Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```