*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*
```// 15```
.
KYAUTATA ZATO KO MUNANAWA
Ni fa ina ganin kamar kyautata zato ko munana shi ba halittaccen abu ne a cikin jikimmu ba, gaskiya sabo ne ko yanayin da mutum kan dauka daga tarbiyyar da ya samu, kodai ta gida ko ta matattara ko makaranta, wannan ko shakka babu in aka matsa wa mutum yakan canja a hankali, sai ka ga in yana son fadin abu sai ya fara kawo togaciya tukun ya ce "Koda yake ni ana cewa na faye kaza da kaza" a hankali sai irin wannan munana zaton ya fita daga cikin dabi'unsa, wani kuma yakan kyautata sakamakon abubuwa amma zama da wasu mutane da lura da yadda abubuwan suke cancanjawa dole ya sauya tunani.
.
Kyautata zato shi ne duk abinda aka ce za a yi sai mutum nan da nan ya yi zaton cewa in sha Allahu sakamakon abin zai zama alkhairi, ba wai yakan qi kallon matsalolin dake ciki ba ne, a'a, yana masa kallon cewa ne ba a riga an fara shi ba, bare a yi masa tunanin cewa wani abu mummuna zai shafe shi, anan kamata ya yi a kalli bangaren kyawun abin sai in an hango wata matsala daganan sai a tsaya a sake lissafi, misali mutum ne ya ce yana sha'awar shiga soja, a zahiri masu buqatarsa a aikin suna yawa, shi kansa yana da hidundumu a gabansa, 'yan uwansa, garinsa, addininsa, qasarsa da sauransu, wannan ya kamata a fara dubawa sai in an hango wata matsala.
.
Wani ne ya kammala jami'a ya ce yana sha'awar noman citta, zaton alkhairi da ya yi wa noman ya qarfafa masa gwiwa, sana'ar citta na cikin abubuwan da ake ce musu gwari, wadanda suke daga mutum can qololuwa, in bai yi sa'a ba su kauce su bar shi ya sha qasa, ya fara noman, ya sayar da abinda ya noma, har ma ya saya a wurin wasu ya sayar, ganin ribar da ya samu sai ya koma sarinta a wurin wasu yana sayarwa, kasuwar ta buda masa, ya canja sana'a, yau yana cikin matsakaitan da ake ganin ba su da tunanin matsalolin yau da gobe, da ya kalli yuwuwar faduwarta da bai fara ba, kuma tana faduwar.
.
Munana zato shi ne duk abinda za a kawo da wahala ka ga mutum ya yi zaton cewa sakamakonsa mai kyau ne, duk abinda aka kawo muninsa yake fara gani kafin kyawunsa, in ya yi magana sai ka ga ya karya wa mutane gwiwa, su yarda cewa abin ba zai yi kyau ba su bari, irin wannan yake damun matasa da dama, hakan kan kurdada bangarori daban-daban na rayuwa, misali mutum ne ya ce zai yi aure, kafin ya fara nema har wani ya ce "Kai! Kana hauka ne? Ba ka da gida ba wata qwaqqwarar sana'a ba aikin gwamnati ka ce za ka yi aure?" Akwai ma wasu 'yan boko da na ji suna zagin qaninsu wai da kwalin digiri ne zai ce zai yi aure?
.
Suka fara jero masa: "Yanzu za ka sha wahala wajen hada kayan auren, da ka gama a yi maganar dakin da za ku zauna, shi ma haya, wata qila ma kuna cikin zamanku maigidan ya ce zai yi amfani da gidansa ku tashi, ko ya ce zai qara tsara fasalin gidan, shekara daya tal matarka ta haihu ga hidimar suna ga nata na haihuwa, komai ya qaru maka kenan, qila kafin ta yaye ka sake yi mata wani cikin, nan da nan a ce na farkon zai shiga makaranta, wata cacar kudin ta kunno kai kenan" ka ji fa! Daga shawarar zai yi aure har an yi masa lissafin shekara 4 don dai a karya masa qwarin gwiwa, in ya biye tasu shikenan an gama.
.
Kwatankwacin wadannan mutanen guda biyu wato mai kyautata zato da mai munanawan kamar ka sami ruwa ne rabin kwalba ka tambaye su, mai kyautata zaton zai ce maka "Akwai ruwa a rabin kwalban" mai munanawan zai ce "Rabin kwalban ba komai" kowa da fuskar da yake kallo, lokacin da ka yi niyyar yin wani abin alkhairi a rayuwarka dole ka hadu da irin wadannan mutanen guda biyu, gaskiya ba muganci ne ko qeta ko rashin sonka da arziqi zai sa su yi maka mummunan zato a kan abinda kake son yi ba, asali wasu mutanen haka suke, duk in za a yi abu ba sa iya kallon bangaren alkhairi, sai dai su kalli daya bangaren kuma su tsaya a kansa.
.
Na ji wanda ya zo neman aure wani gida, sai daya daga cikin uwayen ya fara cewa "To idan kuma wani mummunan abu ya faru da wa za mu yi kuka?" Ba a yi auren ba, ba kuma suna fada da juna ne ba, tsabar munana zato har an fara maganar za a yi saki da qoqarin tunano abinda za a yi in an yi sakin, wani ne ya ce zai yi shago, wani na zuwa ya fara cewa yanzu in aka yi gobara ta ina za a fitar da kayan? Sannan in barawo ya zo cikin dare ya nemi yin kisa ya za a nemi mausu taimako? Sai kuma ya qare da cewa biyan kudin haya kansa matsala ne, duk dai maganganun ba na yabo.
.
In ka ci karo da masu mummunan tunanin ka riqa fassara shi da alkhairi nan take, hakan zai sa su ji a jikinsu su canja, na ji wani yana tambayar abokinsa game da wata qatuwar rukoda da take dakinsa, ya ce "Ina ka kai qatuwar rukodannan taka?" Sai ya ce "Ta yi abinda kake so" da bude bakinsa sai ya ce "Ta lalace?" Ba burinsa kenan ta lalace ba, amma fassarar da ya yi wa maganar kenan, ya munana mata zato, in kana son fara sana'a ko fadadata ka ji masu munana zato kar ka damu sosai, yi maza ka yi mata fassara mai kyau kawai ka nemi yardar Allah SW.
Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```