*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*
```// 17```
.
Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
.
QORON BAKI
Babu wanda ba ya son alkhairi, wani sa'in ko biredi ka je saya sai ka yi sha'awar da ma a ce kamfanin naka ne, akwai lokacin da na je asibiti na ga yadda likitoci suke aiki sai da na yi sha'awar a ce ina cikinsu, duk wani abin sha'awa da mutum ya gani sai ya qaunaci a ce nasa ne, koda kuwa mace ce ta sha kwalliya ta yi irin adon da kake so sai ka ji a jikinka cewa kana so, shi ya sa ma addini ya yi sauri ya kulle wannan babin, wata za ka ga ta sha dogon hijabi da safa a qafa da hannu, ga niqabi ga kamfacecen gilashi, ba za ka taba sanin cewa fara ce ko baqa ba bare ka hade yawu.
.
To irin wancan sha'awar da muke fadi matuqar kana da damar mallakarta yadda za ta koma taka mai zai hana ka fara qoqari? Na sani akwai zarafin da mutum zai fara makarantar muslunci bai hada da boko ba ko kadan ya tafi har jami'a ya tara yara, ga shekaru sun ja sannan ya fara sha'awar zama likita, wanda a tsari sai ya kawo takardar sakandare shi kuma bai san kan lissafi ba, da kamar wuya ya iya cimma burinsa, amma wanda zai iya din wani motsi ya fara? Bai yuwa ga wanda yake son zama likita sai ya fara sanya fararen kaya ya sayi kayan aiki ya shiga asibiti ya ce shi fa yau ya zama likita, ko mai kaciyar yara akwai buqatar gwanancewa da farko.
.
Tunda kana da manufa kar ka yarda tsoro ko kasala da ragwanci su hana ka yin gaba, ko wani walkataccen tunani ko mummunan zato ya sa ka fara dari-dari da abinda kake buqata, na koyar da wata daliba shekaru da dan dama a wani kwaleji, tana da qoqari sosai amma ba turanci, ta gama diploma amma sakamakonta na Education da harshen turancin ya baci sosai, ta karbi shahadarta jiki ba qarfi, amma abin mamaki sai ta koma sakandare jss3, har ta zana WAEC, kafin shekara ta hudu sai ga ta ta zo ofishina ina ta qoqarin tuno sunanta da yake mace ce mai son raha kusan kowa ya san ta.
.
Ban iya tuno sunanta ba, daga bisani ta gaya min sannan amma ta qi magana da ni da Hausa sai da Turanci, nan na sake rikicewa kamar dai ba ita ce wace na sani ba, mace ce matar aure surarta ta qara canjawa ta dan qara qiba ga alamun girma, sai na ce ina ganin ba ke ce wace na sani ba wace nake magana kaza-kaza ta ce wallahi ita ce, zan yi mamaki sai ta gaya min tarihin karatunta da abinda ya koma da ita baya, ta ce yanzu ba ma Larabcin ne a gabanta ba kimiyya za ta karanta, likita take so ta zama, na tabbatar za ta iya, wace ta gama diploma amma ta koma sakandare aji uku don cimma wani buri na tabbatar ba abinda ba za ta iya jure masa ba.
.
Wani kuma za ka iske ba tsoron ne ko ragwanci ba bai son ya kasa cimma burinsa ne, a hakan zai rasa abinda yake so, kamar mai koyon harshe, bai son in ya yi magana a yi masa dariyar abinda ya fada, sai ya gummace ya yi shuru, wani jarumin zai yi ta yi ana masa dariya, cikin dan qaramin lokaci sai ka ga ya iya, akwai wani da na san yana (ta gayu) bala'in son wata yarinya amma ya kasa gaya mata, ita kuma tana ganin kamar irin mutuncinnan ne da suke fadi, 'yan alamun da yake nuna mata ya sa ta qi karbar wani tana jiran ko zai furta, har dai abu ya yi tsawo ta tabbatar ba da gaske yake yi ba ta ba wani dama, har dai aka ba wancan.
.
Saura 'yan kwanaki qalilan a daura auren ya fito yana zagaye-zagaye yana gaya mata cewar ya fi shekara biyu yana son ta, suka yi 'yan koke-koken da za su yi suka haqura, ta je ta yi aurenta a wani gari, abu daya ya wargaza masa shiri, nauyin baki, da a ce ya fito ya fadi da qila ya dasa wata bishiyar soyayya a zuciyarta da za ta riqa girma a hankali, shi ya kasa yi mata magana ne tsoron kar ta ce ba ta son sa, wannan tsoron da yake ji shi ya ja masa yin asarar komai, in dai kana son cin nasara dayan abu biyu ne, ko ka samu ko ka rasa, in ka samu madalla, in ka rasa ka yi karatun da zai ba ka damar kiyaye gaba.
.
Na sha jin mutane na cewa "Da ka yi min magana wallahi da na bar maka, jiya-jiyannan na yi kyauta da shi" wani ya ce "Kash! Me ya sa ba ka gaya min ba? Ai wallahi ban san kana so ba!" Abubuwa da dama wadanda za su nuna cewa tun farko nawan da mutum yake yi wajen fuskantar abinda zai kai shi ga cika burinsa shi ke hana shi cin nasara, da farko tsoron me za ka ji in ka ce wa mace kana son ta ta ce ba ta son ka? Mace ma da shekara sama da dubu daya lokacin kunya na budurwa ta sami Annabi SAW a cikin jama'a ta ce masa ta ba shi kanta ya aura, burinta bai cika ba don Annabi SAW bai nuna yana buqata ba, ba ta yi qasa a gwiwa ba ta riqe wuta sosai sai da ta cimma burinta, rana guda aka ce ta wuce gidan ma'aiki an daura aurenta da shi.
.
Khadija RA ta fito babban gida ne, kuma babbar mace ce, Allah SW ya hore mata abin hannunta, ta sami manyan mutane da suka fito suna qaunarta amma ta qi, sai ga shi ta yi sha'awar auren Annabi SAW duk da cewa yaron gidanta ne a lokacin, ta manta da girman hali da na shekara, ta manta da cewa ita mai hali ce tsakanin manyan mutane, ba ta jira sai an zo nemanta kasancewarta mace wace za a aura ba, tana da manufa kuma tana son cika burinta, cikin ikon Allah 'ya'yan Annabi SAW 7 ne ita ce uwar 6, wannan abinda ya shafi zamanta kewa kenan, hatta a al'amuran saye da sayarwa sau tari sai ka sayar da kaya za ka ji wani ya ce ya dade yana son ya yi maka magana amma bai sani ba ko ba za ka sayar ba, ko sai ka yi wa wasu hanyar daukar aiki a qarshe ka ji wani ya ce yana so amma ya kasa yi maka magana ne.
Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```