HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA 21


*HANYOYIN CIN NASARA A RAYUWA*


 ```// 21```

.
QOQARIN KAWO GYARA

In kana son kawo gyara a ma'aikatarka ko wurin sana'anka na yau da kullum dole ne ka riqa sanya ido, duk kuma wanda ya yi kuskure a gyara masa, sai dai gyarar kan yuwu ne wajen nuna masa kuskurensa, galibin abinda muke yi shi ne in mutun ya yi kuskure a dinga zaginsa da harshe can sama kowa na ji, ko matarka da ka auro in dai za ka juri daga mata murya za a kai lokacin da za ta shiga ramawa, samun mutum a kebe cikin natsuwa gyara ne, yi masa kwarwa cikin mutane kuwa kunyatawa ne.
.
QARFAFA GWIWA DA KALMOMI MASU DADI
In har kana da masu aiki a qarqashinka ka zama mai yawan raha a tsakaninsu amma ta wurin yin amfani da kalmomi masu dadi yadda mataimakanka ba za su damu ba, aqalla za su ruqa dariya ne a duk lokacin da ka cakali wani, irin su "Katafila sarkin aiki" ko "Agogo da aiki aka san ku" da dai sauran kalmomi masu dadi wadanda suke qarfafa gwiwa, to bare kuma in wani sha'ani na gama-gari ya taso kamar Azumi ko Salla babba ko qarama, ka daure a yanka dabba, in babban wuri ne ana samun kudi a raba wa ma'aikata danyen nama, in qaramin wuri ne a yanka rago a soye shi yadda kowa zai ci ya san ya ci nama, wannan qarfafa gwiwa ne, ka yi qoqari ka halarci duk wani taro irin wannan.
.
TA'AZIYYA BIKI KO SUNA
A matsayinka na babba ka daure ka halarci duk wani wurin farin ciki ko baqin ciki na ma'aikatanka, kai babba ne, wannan tabbas ba ja, amma duk wani qaramin da ya gan ka a wurin wani abu nasa zai ji dadi sosai ba kadan ba, masamman abinda ya shafi baqin ciki kamar mutuwa, asarar dukiya da sauransu, to bare kuma a ce ka dan guntsila wani abu ka miqa masa, kar ka raina qanqancin abinda za ka yi, ka duba girman tasirinsa ne a zuciyar wanda ka ba wa, nakan ji ana cewa "Alhaji fa ya zo" wani za ka ji ana cewa "Ai dabi'arsa ce, lamarin ma'aikatansa nasa ne" in da zai yi tunani duk wahalar da suke sha duk da cewa suna samun abin rufin asiri qarshe dai komai wurinsa zai dawo, ba domin gudummuwar da suke badawa ba komai cak zai tsaya.
.
SANYA GASA A TSAKANIN MA'AIKATA
Ka yi qoqarin sanya wata gasa a tsakanin ma'aikatanka, lura da wadannan 'yan bokon, duk da cewa muna kallon su marowata ne, amma abinda suke yi yana yin tasiri sosai a zuciyar ma'aikatansu, sukan yi wasu 'yan alluna a qarshen shekara su rubuta sunan mutum su ba shi a matsayin wata lambar yabo da take jinjina masa a kasancewarsa wanda ya fi kowa zuwa da wuri, ko rashin fashi, ko tsafta, ko ladabi da biyayya, ko aiki tuquru da sauransu, irin wadannan kyaututtuka suna da tasiri ba qarami ba a zukatan ma'aikata, kowa zai yi ta hanqoron a ce ya samu, ba kuma zai samu din ba sai ya aikatu, da haka sai aiki ya bunqasa, to bare a ce ana saya wa mutane motoci da mashina ko talabijin da wayoyin hannu da sauransu.
.
Wanda bai samu kyauta ba bai dage ba kenan, in babban kamfani ne ko saudiya sai a kai wani, duk da cewa mutum daya ya samu, amma zai zaburar da sauran ma'aikatan idan suka ji cewa dagewarsa ce da jajurcewa silar samun kujerarsa, in qaramar ma'aikata ce za a iya saya wa talaka qaramin buhu na shinkafa, ko galan din manja ko na man-gyada, ko dai wani abinda zai jawo hankalinsa, wannan ya fi masa wata lambar yabo, da yawammu ba mu san qimarta ba, ba mu cika wani lura da cewa nan da nan za mu murtsuke ci ya qare kenan ba.
.
DORA WA MUTANE NAUYI
Ita kuma wata dabi'a ce mummuna da ta zama dole mutum ya guje ta a matsayin shugaba ko abokin aiki, za ka taras wani kullum cikin hanzari ne "Don Allah wane dan riqe min wuri kaza ina son na yi kaza" ko ka ji yana cewa "Don Allah yau ba zan sami damar zuwa ba amma wane dan kama min kaza" in hakan ya fara yawa ko ka nema ba mai kula ka, za ka taras duk wanda ka kama yana zillewa saboda an maimaita ba daya ba ba biyu ba, ko shugaba ne ya yawaita dora wa ma'aikatansu wasu ayyuka a wajen abubuwan da suka san sun zama musu dole tabbas za ka taras sun noqe, ko in suka ji motsinsa kowa ya kama gabansa, ba laifi ya faru sau daya ko biyu amma ba a hade ba kuma kar ya yi tsawo, in ka dora wa mutane aiki to yagar musu wahalar aikinsu ka matsa su karba koda sun qi, shi ne zai ba ka garantin ka nema wata rana.
.
Idan kuma ka shugabanci wani bangare na jama'a a cikin ma'akata, taka ce ko aiki aka ba ka, ka yi qoqari wurin tabbatar da an yi aikin cikin nishadi, a maimakon ka zabo wanda ka raina ka labta masa kaya ka jira ya yi shi kadai, yi qoqari ka kira taro, koda ka san yadda za a yi ka dan dakata, ka fito da aikin sarari, ka nemi shawarar abokan aikin naka kan yadda za a tafiyar da shi, a maimakon mutum guda ya yi shi kadai, wanda hakan kuma zai dauke shi wani dan lokaci, ka yi qoqari ka kasa musu yadda kowa zai yi da kyau, kuma cikin nishadi sannan a dan qanqanin lokaci, buqata ta biya kenan, sannan shugaba ya riqa samun lokaci yana zaunawa da ma'aikatansa yana tattaunawa da su.
.
Abinda ya fi komai mahimmanci ma ya riqa shiga cikin aikin, in zai yuwu kar ya bari a sami wani bangare na kamfanin wanda ba ya shiga a yi da shi ko a ce bai san kansa ba, wannan sifar shugaba na qwarai kenan wanda tabbas nasarar yake nema kuma aiki yake yi tuquru don isa gare ta, ba wai mutum ya yi ofishi a gefe sai dai a riqa kawo masa takardu yana cikewa ko tattaunawa da abokan ciniki ba, na yi karantarwa a wata makaranta wace hedimastan lokaci-lokaci yakan hutar da wani malami shi zai koyar don ya ga fahimtar 'yan ajin da duk inda suka tsaya a karatunsu, dan lokaci kadan za ka gan shi a qofar tagarka yana kallon abinda kake yi wa daliban, in ya ga kuskure za ka ji kira a ofis, ya gyara maka cikin tsanaki.


Rubutawa:- Baban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf ja'afar Kura 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

 ```Ga masu sha'awar Shiga Zauren MIFTAHUL ILMI WhatsApp sai a aiko da cikakken suna ta WhatsApp zuwa ga lambar Mu 07036073248```
Post a Comment (0)