SHARHIN FIM ƊIN SRIMANTHUDU
Srimanthudu fim ɗin kudanci India ne da aka fitar a shekara ta 2015. Fim ne da ƙunshi abubuwa da dama waɗanda in muka shiga cikin sharhin da kyau za ku fahimci hakan.
Bada Umurni - Koratala Siva
Ɗaukar Nauyi - Y. Naveen, Y. Ravi Shankar, C. V. Mohan &
Mahesh Babu
Rubutawa - Koratala Siva
Sautin shiri - Devi Sri Prasad
Horas da 'Yan Wasa - R. Madhi
Tacewa - Kotagiri Venkateswara Rao
Kamfanin da ya shirya - G. Mahesh Babu Entertainment Pvt. Ltd & Mythri Movie Makers
Yaɗawa - Eros International
Ranar Fita - 7 August 2015
Tsawon Shiri - 158 minutes
Ƙasa - India
Harshe - Telugu
Kasafi - ₹400—700 million
Kasuwancin Box office - ₹1.4—2.0 billion
Da fari an shirya cewa fim ɗin Srimanthudu zai samu shiryawa ne a ƙarƙashin kamfanin UTV Motion Pictures, amma daga baya sai kamfanin ya cire hannunsa daga aikin saboda banbancin ra'ayi aka samu. An fara ɗaukar wannan shiri ne a ranar 11 ga watan Agustan 2014 a Ramanaidu Studios da ke Hyderabad. Ko da yake mafi yawancin fim ɗin an ɗauke shi ne a Hyderabad, wasu sassan shirin an ɗauke su ne a Pune, Tamil Nadu da kuma Malaysia.
Srimanthudu da kuma fassarar shi da aka yi da harshen Tamil mai suna Selvandhan duka an sake su ne a rana guda a duniya baki ɗaya. Masana da masu sharhi sun yabi wannan shiri sosai, yayin da su ma 'yan kallo suka yaba wa fim ɗin ta hanyar ci gaba da kallonsa har sai da ya zama fim ɗin Telugu na uku da ya fi kowanne kawo kuɗi.
Bayan fitar wannan fim, Jarumai, ma'aikata da 'yan siyasa sun bayyana tsari da burin taimakawa ƙauyuka tare da taimakon mutanen ƙauyen da ke yankin Telangana da Andhra Pradesh. An fassara wannan fim izuwa harshen Hausa da sunan Mai Arziƙi.
Labarin Shirin
Harsha Vardhan shi kaɗai ne ɗa kuma magajin kamfanin kasuwancin mahaifinsa Ravikanth wanda ya kai kimar biliyan ₹250. Bayan ya haɗu da Charuseela a bikin zagayowar ranar haihuwar abokinsa Apparao, sai ya shiga jami'a inda ya fara koyon ilimin haɓaka ƙauyuka. Burin Charuseela shi ne ta hi amfani da kimiyya da fasaha wajen taimakawa ƙauyen Devarakota da ke Uttarandhra wanda can ne tsatsonta. Da fari dai abota ce ta shiga tsakaninsu da Harsha, amma da tafiya ta yi nisa kuma sai abin ya koma soyayya.
Baki ɗayan albarkatun ƙauyen Devarakota suna ƙarƙashin ikon wani tantiri ne mai suna Sashi, wanda ya kasance ɗan uwa ne ga Ministan tsakiya wato Venkata Ratnam wanda shi kuma zaluncinsa ya sa 'yan ƙauyen da dama yin hijira zuwa birni domin samun sauƙin rayuwa.
Sai dai duk da haka, shugaban wannan ƙauye wato Narayana Rao ya kasance mai fata tare da burin ganin ci gaban wannan ƙauye da mutanen cikinsa. A gefe guda kuma ɗan Ratnam wato Radha ya yi barazanar cin zarafi da mutunci ga ahalin Ravikanth matuƙar bai janye daga neman wata ƙwangilar gina hanya ba. Ashe ɗan ƙanwar Ravikanth wato Karthik, wanda ke burin ganin ya gaji Ravikanth shi ne ya ba wa Radha muhimman bayanan kwangilar, amma sai Harsha ya gano hakan. Bayan ya yi wa Ratnam gargaɗi akan hakan, sai Harsha ya shigar da takardar neman wannan kwangila a sirrance ba tare da mahaifinsa ya sani ba kuma aka samu kwangilar.
Yayin da Charuseela ta fahimci cewa Harsha ɗan Ravikanth ne, sai ta fara Ja baya da shi. Da ya tambaye ta dalili, sai ta ke bashi labarin cewa mahaifinsa ɗan asalin ƙauyen Devarakota ne da ya shigo birni domin ya tara dukiya, ba kamar mahaifinta ba wato Narayana Rao wanda ya zauna a ƙauyen domin ya taimaka musu. Daga nan sai ta yi masa bankwana ta tafi.
Bayan ya nemi dogon hutu a wajen mahaifinsa kafin fara shiga ofishinsa, sai Harsha ya tafi ƙauyen Devarakota ba tare da sanin mahaifinsa ba. A ƙauyen Devarakota ne ya haɗu da Rao inda ya gabatar da kansa a matsayin ɗalibi mai karantar hanyoyin haɓaka ƙauyuka kuma ya zo ƙauyen ne domin yayi nazari akansa. Bayan ya nazarci ƙauyen Devarakota da kuma irin zaluncin Sashi da kyau, sai Harsha ya bayyana cewa zai ɗauki nauyin ƙauyen tare da haɓaka shi. A dai-dai lokacin da yake ƙoƙarin haɓaka ƙauyen ne kuma sai Ratnam ya umurci Sashi da ya haɓaka ƙauyen saboda su samu cin zaɓe, amma sai ya yi biris bisa tunanin cewa ya za a yi kura da shan bugu gardi kuma da kwashe kuɗi?
A dai-dai wannan lokaci ne kuma Harsha ya gano cewa a lokacin da Ravikanth yake matashi shima ya so ya haɓaka wannan ƙauye kamar yadda Harsha ke yi a yanzu. Amma sai Ratnam da Sashi suka ƙulla makaircin da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama, inda hakan yasa aka ci mutuncinsa kuma aka kama shi. Wannan dalili ne ma ya sa ya bar ƙauyen ya koma birni har ya zama attajiri.
Yayin da Charuseela ta dawo ƙauyen Devarakota ta ga aikin da Harsha yake yi, sai ta yi tunanin cewa ya zo ne domin ya shawo kanta da na iyayenta domin ya aure ta. Amma a hankali sai ta ji ya burge ta bayan ya magance wata matsala da ta taso a cikin gidan. Daga baya sai Harsha da Charuseela suka fahimci cewa Ratnam yana shirin mallake dukkan filaye da gonakin ƙauyen saboda wata harƙallar siyasa da ya sa a gaba. Hakan ya sa Harsha ya je ya ja masa kunne akan ya fita daga harkar aikin da yake yi a wannan ƙauye.
Harsha kuma sai ya kai ziyara zuwa wata ma'aikata ruwan kwalba wanda bayan samar da giya da suke yi a sirrance, suna kuma kwashe kaso mafi tsoka na ruwan wannan ƙauye wanda shi ne mutanen ƙauyen ke amfani da shi. Da yayi ƙoƙarin rufe shi, sai yaran sashi suka kawo masa farmaki inda har suka ji masa rauni aka kai shi asibiti.
Shi kuma Ravikanth, da yake an bashi labarin aikin da Harsha ya fara a wannan ƙauye na Devarakota, sai ya yi ƙoƙari ya dawo da Harsha Hyderabad, inda ya shiga ofishinsa bayan ya warke.
A wata zazzafar tattaunawa da suka yi ne dai Ravikanth ya amince wa Harsha da komawa ƙauyen Devarakota, wanda hakan ya sa ya samu soyayyar Harsha, abinda ya daɗe yana nema. Harsha sai ya miƙa ragamar kasuwancin baki ɗaya wa Karthik daga nan ya tafi.
A ƙauyen Devarakota, Harsha ya kashe Ratnam da Sashi a wata ma'aikata amma sai ya tsara abin a matsayin tsautsayi ne kamar yadda suka yi wa mahaifinsa. Fim ɗin dai ya ƙare ne a yayin da aka nuno Ravikanth da ahalinsa sun kai ziyara wa Rao a bikin
Sankranthi inda Harsha da Charuseela suke zaune a matsayin mata da miji.
Jaruman Shirin.
Mahesh Babu - Harsha Vardhan
Shruti Haasan - Charuseela
Jagapathi Babu - Ravikanth
Rajendra Prasad - Narayana Rao
Sukanya - mahaifiyar Harsha
Sithara - mahaifiyar Charuseela
Mukesh Rishi - Venkata Ratnam
Sampath Raj - Sashi
Harish Uthaman - Radha
Vennela Kishore - Apparao
Sriram Edida - Ɗan uwan Narayana Rao
Tulasi - Surikar Narayana Rao
Subbaraju - Ɗan uwan Ravikanth
Rahul Ravindran - Karthik
Ali - Rajaratnam
Sravan -
Sivaji Raja - Suryam
Ravi Prakash - Dr. Ganesh
Surya -
Tejaswi Madivada - Yarinyar Venkata Ratnam
Surekha Vani - Sumathi
Anand -
Sanam Shetty - Meghna
Angana Roy -
Ravi Varma -
Nikkita Anil Kumar -
Poorna - fitowa ta musamman
Waƙoƙin Shirin
1. "Rama Rama"
2. "Jatha Kalise"
3. "Charuseela"
4. "Srimanthuda"
5. "Jaago"
6. "Dhimmathirigae"
©️✍🏻
Jamilu Abdurrahman
(Mr. Writer)
+2348185819176
Haimanraees@gmail.com