*💝🌹//YAREN SOYAYYA 006//🌹💝*
*_Mawallafi:- Dr Abdulkadir Ismail Kano_*
*_BALAGURON RAYUWAR AURE:_*
Allah Ya yi tsari a rayuwa cewa babu wani abu da zai dawwama a yanayi guda, komai Yana canjawa daga lokaci zuwa lokaci, Kuma wannan canjin yana nuna cikar kadaitakar ALLAH Wanda baya canjawa Shi kadai, dukkan wani abin halitta mai canjawa ne. ALLAH Ya bayyana halittar mutum da cewa:
*_( اللَّهُ الَّذِي خَلَقَكُم مِّن ضَعْفٍ ثُمَّ جَعَلَ مِن بَعْدِ ضَعْفٍ قُوَّةً ثُمَّ جَعَلَ مِن بَعْدِ قُوَّةٍ ضَعْفًا وَشَيْبَةً ۚ يَخْلُقُ مَا يَشَاءُ ۖ وَهُوَ الْعَلِيمُ الْقَدِيرُ )*_
*(ALLAH ne Ya halitta ku daga rauni, sa'an nan Ya sanya wani ƙarfi a bayan wani rauni, sa'an nan Ya sanya wani rauni da furfura a bãyan wani ƙarfi, Allah na halitta abin da Ya so, kuma Shĩ ne Masani, Mai ĩkon.) [Rum:54]*
Wannan tsarin shi yake bin dan-adam aduk rayuwarsa, rauni, sannan bayan rauni a samu karfi, sannan bayan abu yayi karfi rauni ya sake kama shi wani lokaci har ya tsufa ya rududduge. kamar haka rayuwar aure take farawa, da karsashi da marari da doki, sannan al’amura su fara ja da baya, sannan wani lokaci su sane baki daya komai ya zama lami. Kuma wannan itace dabi’ar duk wani abu na duniya.
*_Kamar yanda Manzon ALLAH (ﷺ) ya bayyana mana acikin Hadisi:_*
*”حَقٌّ عَلَى اللَّهِ أَنْ لاَ يَرْتَفِعَ شَيْءٌ مِنَ الدُّنْيَا إِلَّا وَضَعَهُ “*
*_“Alkawarin ALLAH ne cewa; Babu wani abu na duniya da zai daukaka sai ALLAH ya dawo dashi kasa.”_*
A bisa wannan fahimta, Malamai masana halayyar dan-adam, da Kuma lura da lamura sun bayyana matakai na haduwar mutum da matarsa, tun Yana alakar tana jaririya har ta girma har Kuma ta tsufa kamar haka:
*_Matakin Farko:- MAGANADISU-*
Da larabci sukan kira shi da *_(مرحلة الانجذاب)_*, da turanci *(Infatuation Stage)*, wannan mataki yakan zamo kamar yadda mayen karfe yake janyo karfe, matukar sunyi arbu, to sai ya janyu zuwa gare shi. Maganadisunsa zai fizge shi, ba tare da yayi la’akari ba, ba tare da ya shirya ba, kwatsam sai ya ji shi ya kamu. shiyasa ake cewa: Ciwon soyayya ya kama shi, ya fada cikin kogin soyayya, soyayya ta fizge shi, ya kamu, da dai sauran kalmomi da ake amfani dasu. irin haka zaka ji a harshe kamar larabci sai ace: *(وقع في الحب، شغفه الحب*) da sauran su, a turanci ace: *_(Falling in Love)_* ma’ana dai mutum fadawa yayi, idan kuwa akace mutum ya fada, to ma’ana bai shirya ba, an debe tsammani, Bai yi zaton abin zai bayu zuwa ga hakan ba.
Soyayya wata kalma ce da masana suka ce tana da fadin gaske, tana da zurfin gaske Wanda hakan ya Sanya tana da wahalar fahimta ko iyakancewa acikin wadansu kalmomi. Wannan ne ma ya Sanya suka ce babu wani malami da ya taba yin ta’arifin soyayya Kuma yaci nasarar iya bayyana ta ba tare da wani tasgaro ba.
Ita soyayya wani abu ne da mutum yakan ji a zuciyarsa na Yana son ya fadada kansa, ya Kara buda kansa ya Kara yawaita kansa ta hanyar kamfato wani zuwa gare shi. Yayin da mutum yake son wata ko wata take son wani, kamar tana so ne ta fadada kanta don ta karu ta habaka, Kuma har ta wanzu tsawon lokaci.
A irin wannan yanayi ne zaka samu nau’in soyayya iri-iri, kamar shakuwa, domin rabuwa wani nau’i ne na rage fadadar mutum, zaka samu tsoro akan wani abu kamar 'Da, saboda shima wani bangare ne na fadadar mutum, haka kishi akan Mata ko mace akan mijinta, saboda kaucewa tuntube da wani zai yi don ya yafi ce shi, da misalai irin wannan. Wannan yake bayyana cewa akwai bambanci tsakanin fadawa cikin soyayya, ko kamuwa da soyayya da Kuma ita soyayyar kanta, domin a yayin da mutum yake kokarin fadada shi da kansa ne yake hobbasa, Kuma ya Sanya himma, Amma faduwa kuwa bashi yake yi ba, samun kansa yake yi a ciki.
*A bayanai masu zuwa za mu yi kokarin bayyana wannan bambanci.*
*_Zamuci gaba Insha Allah_*
*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*