YAREN SOYAYYA 05


*💝🌹//YAREN SOYAYYA 005//🌹💝*

 *_Mawallafi:- Dr Abdulkadir Ismail_*

 *_9- Kare Al`umma Daga Lalacewa Da Sakwarkwarcewa_*
  Rashin aure na janyo yaduwar alfasha, yaduwar alfasha na sanya samar da `ya`ya da ake Haifa ba tare da tabbatatun Iyaye ba. Idan yaro ya zamo bai san mahaifinsa ba, yakan taso ne cikin matsalar rayuwa, kuma uwar ta sa takan kasance cikin matsananciyar wahala wajen kula da shi, da kokarin faranta masa.
  A qasar Iran a yau akwai tattaunawa mai zafi tsakanin masu ganin a ci gaba da barin Mut'ah na gudana da kuma masu ganin cewa dole a tsayar haka. Dalilin masu ganin lallai dole a tsayar da yin Mut'ar ya hada da; yaduwar yara da ake kiran`ya`yan titi, wadanda ba su dangantuwa da kowa. Hakan ya sanya su sun tsunduma cikin aikata muggan laifuka masu hatsarin gaske, kamar kisa da sata da fesa sinadarin Acid a fuskar mata masu fitowa da ado, da kashe mata masu zaman kansu. Sannan barin Mut'ar ya qara sanya mazaje suna iya fita waje su biya buqatarsu ba a wajen matansu ba, kuma sakin aure ya yawaita, kuma idan aka yi sakin, mace sai ta shiga harkar Mut'ah gadan-gadan don ta iya ci da kanta.
  Rashin samun nasaba tsakanin da da wanda ya yi dalilin samuwarsa yana haifar da rugujewar tsarin iyali da zamantakewa, ya yanke alaqa tsakanin `yan uwa ta yadda dangi ba za su yarda da dan da ba a san ubansa ba, yana je fa yaro cikin mummunar tarbiyya, ya batar da nasabar mutum, kuma yana sanyawa a baiwa wani haqqin da bai cancanta ba wajen gado, wadannan da ma wasu dalilan duk sabubba ne na sukurkucewar al`umma baki daya, kuma wannan kadai na tabbatar da muhimmancin sanin manufar aure a Musulunci.

*_10- Kare Al`umma Daga Cututtuka Masu Fatattakar Zamantakewar Al`ummah_*
   A yau bai zama abu boyayye ba cewa cututtuka masu kacalcala al`umma suna yaduwa kamar wutar daji, cuta mai karya garkuwar jiki (AIDS) cutar ciwon sanyi, cutar neman kananan yara, cutar jinsi daya da sauransu suna ta yaduwa saboda mutane suna son su biya buqatarsu wadda Allah ya halitta musu ba ta han-yar aure ba. Yin aure na kare al`umma baki daya daga wannan annoba da take yaduwa ta cututtuka, tabbaci ne na kashedin da Manzon Allah ﷺ yayi mana inda ya ce:-

”خَمْسُ خِصَالٍ يَا مَعْشَرَالْمُهَاجِرِينَ أَنْ تَنْزِلَ بِكُمُ أَعُوذُ بِاللَّهِ أَنْ تُدْرِكُوهُنَّ: لَمْ تَظْهَرِ الْفَاحِشَةُ فِي قَوْمٍ قَطُّ حَتَّى يُعْلٌنُوا إِلَّا فَشَا فِيهِمُ الطَّعُونُ والأَوْجَاعُ الَّتِي لَمْ تَكُنْ فَشَتْ فِي أَسْلَافِهِمْ.“

  ``Ya ku taron Muhajirai (wadanda suka yi hijira)! Abubuwa biyar idan aka jarrabe ku da su, kuma suka sauko muku- ina neman Allah ya tsare kada ku riske su: alfasha ba za ta taba bayyana ba cikin wata jama'a har su bayyana ta sai cututtuka wadanda a da ba asansu ba sun bayyana a cikinsu....``.
   Abin fahimta a wannan gaba shi ne:- mutum ya zauna ya yi karatun ta nutsu a kan dalilin da ya sa zai yi aure, kuma ya sanya wannan burin basa a gaba don qoqarin cimma wannan burin, irin yadda mutum yake neman kudi ko karatu ya fadi ko ya rasa a wani lokacin, umma wannan ba ya sanya shi ya ce ya fasa, sai dai ya qara kaimi da gyara kus-kure. Wani manufarsa za ta iya zama gaba dayan abin da aka ambata ne da kari wani kuma wani bangare ne daga cikin abin da aka ambata, amma dai a fahimci cewa aure a Musulunci ba kawai ta-more ba ba ne, a,a akwai manufofi masu tarin yawa a ciki wadan da sukan zama linzami daga kaucewa daga kan hanya ta daidai.
   Wadannan manufofi na aure da Musulunci ya tsara, dukkansu masu muhimmancin ne, da ace don soyayya kadai ake yin aure da kuwa an tozarta abubuwa da dama, daga ciki idan mutum ya ga cewa shi ba ya jin soyayya a cikin zuciyarsa, sai ya sanya qafarsa ya fice daga cikin gidan aure, ya bar yara da aka haifa a tozarce. Sai kuma ta fita ko ya je ta qara aure, ta qara rasa soyayya sai ta sake ficewa ta sake tozarta yara don kawai biyan buqatar zuciyarta. Wannan dalilin ne ya wajabta wa mutum a matsayinsa na Musulmi ya san cewa aure na da manufofi dama ba lallai soyayya kadai ba, kuma ya yi iya qoqarinsa don kare wannan manufar don samar da al`umma ta gari.

*_Zamu cigaba Insha Allah_*

*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*
Post a Comment (0)