*_💝🌹//YAREN SOYAYYA 008//🌹💝_*
*_Wallafar:- Dr Abdulkadir Ismail Kano_*
*_Mataki na uku: HADEWARJUNA:_*
A wannan mataki ne mutum yake yanke shawarar cewa yana son ya kasance da Wanda yake so har abada ta hanyar yin sure. Saboda wannan sinadari na maganadisu da yake tare dasu yana jansu. Da za'ayi kokarin hana su yin wannan aure, sai su fandare, ko su nemi halaka kan su, ko su sami tabin hankali, ko su hadu da mummunan tashin hankali.
Bayan an zama daya, sun tare a sabuwar shekarsu, sai dukkan su suyi kokarin boywa juna aibin juna, ma’ana bata son ya ganta dagajaja, shima ya zama dan tsaf-tsaf da safe, ya sanya turare, ya goge hakora da safe, zata yi gaggawar tashi don ta danyi shafe-shafe, ya shirya abinci, ta share gida ta kimtsa komai. Shi kuma a bangarensa zai yi iya kokarinsa don ya nuna jarumtakarsa. Da zata nemi a sayo wani abu idan ya fita, to zai kawo, koda kuwa sai yaje yayi rance ne, wani lokaci ma don ya burgeta zai kawo kafin ta tambaya.
Yakan iya bada uzuri akan wani abu da yasan ba daidai bane, Saboda kada ya bata mata, kuma har zuwa wannan lokacin mutum yana kokarin ganin daidanta, ya gimtse ido ga duk wani kuskurenta ya bada uzuri akan sa, haka itama take kokarin tayi, tana fassara wani abu da yake mata a matsayin soyayya, da za ta ga ya nuna tsananin kishinsa akan wani idan yana kallonta, sai taji dadi domin a wajenta wannan alamar kauna ce.
Wannan mataki shine yafi kowane hatsari, bayan an hadu an yi aure, to wadannan sinadarai da suke shawagi tsakanin juna sun zo kusa, kuma an San juna sani na kusa, sannan kuma an ga juna gani na kusa, anyi arba a yanayin da babu kwaskwarima mai yawa, amma duk da haka karfin wannan sinadarai za su ci gaba da aiki gwargwadon karfin su, sannan bayan nan su fara dusashewa, karfin shawaginsu ya fara raguwa.
Wani lokaci, saboda al’ada da kuma wani tsari na daban sukan bude kwalbar wannan sinadarin har ya sulale da wuri, duk da cewa wannan abu ne da yake bukatar wani bayani na daban mai dan fadi a wani tsari na daban.
*_Labari:-_*
Sun yi aure irin na saurayi da budurwa, kuma da kaunar juna da mararin juna, da kuma...
*_Zamu cigaba Insha Allah_*
*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*