YAREN SOYAYYA 09

*💝🌹//YAREN SOYAYYA 009//🌹💝*

*_Wallafar Dr Abdulkadir Ismail Kano_*

*_Domin fahimtar wannan labarin zanso makaranta su koma baya su dan karanta rubutun mu na jiya kamin su karanta labarin-nan_*

              *_Labari:_*
   Sun yi aure irin na saurayi da budurwa, kuma da kaunar juna da mararin juna, da kuma kokarin faranta wa juna. A irin wancan lokacin na da, rediyoyi manya ba a kowane gida suke ba, amma shi Allah Ya bashi iko ya sayo katuwar rediyo kirar Sanyo mai sifika har biyu; hagu da dama, ga gidansa dan karami daidai kana’a. A irin zamantakewa irin ta da, matar nan takan ta shi ta goge ledar dakinta, ta wanke ban daki, ta kai ruwan wanka, kafin ya fito ta ajiye masa abincinsa ta rufe shi da tuma-kasa, ta koma gefe tana kallonsa yana cin abincinsa, kuma tana sauraren ko akwai wani abu da zai bukata.
Wata rana bayan ya tafi neman abincinsa, lokacin ta zarta wata biyu a gidan, sai hali irin na mata ya motsa mata, sai taga bari ta wanke gidan, ta sake jeren kayan kwalla da kumbo da yake cikin dakinta. Ba tare da taimakon kowa ba, ta fito da kayan dakinta, dama a wancan lokacin ba masu yawa bane, sannan ta wanke dakin ta fito ta wanke kwanukanta ta Shanya. A wannan lokacin ne taga ya kamata wannan rediyon nasu ma a wanke, haka kuwa ta sanya sabulu da soso ta wanke wannan rediyo tatas ta kai rana ta shanya.
Yayin da mijin ya dawo bayan rana ta karya, sai yaga gida ya canja, anyi shanya a tsakar gida, cikin farin ciki ta tambaye shi ra’ayinsa, ya kuwa yabawa kokarin ta, yayi murna, tace masa ai har rediyon can sai da na wanke da soso da sabulu, Yace: “A’a! a’ahh!! Har rediyon ma sai da kika wanke?” Ta tabbatar masa ya kara yaba mata. Amma shi a masaniyarsa ya san cewa an tafka kuskure, saboda rediyo bata son ruwa.
     Yamma ta yi aka hada komai aka sake jerawa, aka kunna rediyo, a wannan lokacin ne rediyo ta ce: Ai na kurumce na bebence. Suka yi suka yi don ta yi magana taqi. Shi da ma yasan a-rina, amma dai don ya faranta mata suka yi ta kici-kici don su ji sauti abu ya ci tura. Daga nan sai ya ce: Watakila akwai wani abu da ba mu gane ba, saboda haka an juma zan kai wa Mai gyara ya taba mana. Haka ya fita da rediyo aka gyara. 
   Bayan shekaru da zamantakewarsu ne matar ta gane cewa ashe yana sane bai yi mata inkarin wannan kus-kuren da ta tafka ba, daga baya sai abu ya koma tsokana: ``Miko min soso da sabulu mu wanke rediyon nan`` Sai ya zama abin kakaci tsakaninsu bayan shekaru sun yi nisa. 
   
   Wani zai yi zaton wannan labarin almara ne, amma kuma wanda abin ya faru da shi yana nan a raye, auren na su ya zarta shekaru talatin yanzu haka suna tare.

*_TAKAI-TACCEN SIFFAR WANNAN MATAKI:-_*

   - Marari da Qaddara juna
   - Haduwar juna da sanin hakikanin juna a aikace
    - Kaddara juna da kokarin biya wa juna buqata
    - Bai wa juna uzuri a kan abin da ba daidai ba
    - Qokarin fitowa a sifa mafi kyau a halitta da dabi'a ga juna.

*_MATAKI NA HUDU:- SABAWA_*

*Zamu tsaya daga nan sabida gobe mu tashi daga farkon wannan mataki (Na biyar) zuwa Qar'shen sa Insha Allah*

*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*

Post a Comment (0)