YAREN SOYAYYA 10

*_💝🌹//YAREN SOYAYYA 010//🌹💝_*

*_Wallafar:- Dr Abdulkadir Ismail Kano_*

*_MATAKI NA HUDU:- SABAWA:_*
   Wannan mataki ne da yake biyo bayan matakin hadewar juna. Bayan an zama daya a gida daya, a wajen kwanciya daya, a wajen tunani an zama daya. sai Kuma wannan mataki yazo na sabo, ta yadda dukkanninsu za su fara aikata abin da suka saba yi ne kawai, su fara saba fadin abin da suka saba fada yau da kullum. Ma’ana sabunta lamurra tsakaninsu da yiwa juna bazata da wani abin burgewa zai ja da baya, ya zama abinda suke yiwa juna ya koma kamar wannan nauyi ne a wajibi da mutum yake kokarin saukewa kawai.
Idan a wancan mataki na maganadisu da kokarin fahimtar juna, kullum tunaninsa me zai yi don ya shawo hankalinta, to a wannan matakin babu wannan tunanin acikin kundin karatunsa. Idan a waancan matakai tana tunanin me zata yi na abinci ko ado don tayi masa bazata, to a wannan matakin ba zai ga haka ba, idan a wancan matakin idan ya fita waje kwakwalwarsa na fada masa cewa ya kamata ya sayo wani abu da yake bata sha’awa, to a wannan mataki burinsa shine menene abu na lallai-lallai da ake bukata ya kawo.
Zai iya tashi da safe ya Kai har karfe sha biyu da kayan barci a jikinsa ba tare da ya damu yayi wanka ko ya wanke bakinsa yayi kwalisa ba. Haka ita ma zata iya tashi ba tare da ta shirya ba, har ma ya zama ya zama tana da kayan aikin gida, a lokacin da maigidan yake nan, ba zata fara tunanin wanka ba har sai ta gama aikin gida baki daya, tayi shara, tayi girki. Sai ta fara sabawa da Yanayin da yake ciki, shima ya daina damuwa da Yanayin da take ciki, ko tayi kwalliya ko ta Sanya turare duk Bai damu ba.
Amma wannan bazai hana shi damuwa da kuluwa ba idan ya ga tayi ado zata fita unguwa. Kuma ita ma nan da nan zata tunzura idan taga yayi wata magana cikin tausasa murya, tare da cewa dukkanninsu suna aikata irin wadannan abubuwa suna ganin ba komai bane, tare da cewa dukkansu sukan yi watsi da abubuwan da suke ganin zasu kyautata zamantakewarsu a mataki na daya da na biyu, amma Kuma wannan bai hana su jin zafin abin da ita take yi masa ba, haka shi ma Yana kufula da abin da yake gani tare da ita na rashin kulawa da kanta ko da shi.
Yayin da Ma’aurata suka kawo wannan mataki, a wannan lokacin ne dukkansu sun gina wani tsari na tunani akan junansu. Ya yi wa kansa hukuncin cewa ga abin da zata yi masa, ga irin maganar da zata mayar masa ko ta bashi amsa idan yayi mata wani abu, ga irin Muhimmancin da za ta baiwa abin da ya fada ko rashin muhimmanci. Daga nan sai ya Gina hukunce-hukuncensa kanta a bisa abin da ya gina na fahimtar ta a kansa, Wanda duk hakan ba lallai ya zama haka abin yake ba, amna dai shi ko ita a kan haka suke yin hukunci.
Misali zata fada masa cewa tana so a kaita dubiya marar lafiya karfe hudu na yamma, amma bai zo ba har sai da Magariba ya dawo. Farkon tunaninta shi ne Bai damu da ita ba, shi yasa ya manta da wannan al’amari, da a lokacin da yake son ta ne da Bai manta ba. Shi ma da zai fada Mata cewa zai zo da abokansa Yana son ayi musu wani abu na daban, sai yazo ya tarar ta manta, to fassararsa ita ce, da ma bata dauke shi da muhimmanci ba, shi yasa tayi wasarere da umurnin.
Da zai yi Mata abin da bata zata ba, kamar ya sayo Mata wata atamfa ko wani abu da take tsananin so, sai wannan abin ya kidimata don farin ciki, saboda ita a wannan matakin bata zaton ya damu da ita ballantana yayi Mata irin wannan abu. Haka shima da zai dawo da dare ya tarar tayi masa wani shiri na daban sai ya fara tunanin ko wani abu ne ya faru, ko Kuma tana da wata bukatar da zata tambaye shi yayi Mata, daga nan sai ya Sanya shakka acikin zuciyarsa.
Idan ma’aurata suka zo wannan mataki, shi ne suke Sanya wa kan su wata fahimta ta zama da abokin zamansu. Da yawa zaka ji idan an tambaye ta game da wani abu za ta ce: “Ai na san ba zai yarda ba” Ma’ana ta gamsu da fahimtar da tayi a kansa na cewa ga abin da zai iya yi ga abin ba zai iya ba. Haka shima zai Gina fahimtarsa a kanta. A irin wannan yanayi ne, idan mutum ya gane dan-uwan zamansa, ko dai ya karbi halayyensa kamar yadda yadda yadda, sai yaci maganin zama da shi, ko Kuma ya yi ta damun kansa wajen sai ya canja shi akan abin da bazai canja ba.
A irin wannan matakin ne sukan fara tunanin ko dai zaben tumun dare suka yo, ko Kuma su kudurce cewa yaudararsu aka yi, daga nan sai su shiga mataki na biyu. A tsarin soyayya da suka dauko a matakin Farko babu sharadin cewa lallai sai abokin zamana yayi daidai da irin ra’ayin da nake Kai zan cigaba da zama da shi, Amma da yake tafiya ta fara nisa, sai mutum ya fara tunanin dole sai an canja sannan za a sami gamsuwa.
*_TAKAITACCIYAR SIFFAR WANNAN MATAKI:-_*
● Gina hukunci a kan abin da kowa yake zaton zai yi, ko za a yi masa.
● Yin abu na wajibi kawai, tare da yin ko oho ga abin burgewa ko farantawa.
● Rashin damuwa da ado ko bajinta ga abokin zama.
● Ganin cewa duk an zama daya, babu bukatar wani abu na musamman ga juna.

*_Zamu cigaba Insha Allah_*

*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*

Post a Comment (0)