YAREN SOYAYYA 13

*💝🌹//YAREN SOYAYYA 013//🌹💝*

 *_Mawallafi:- Dr Abdulkadir Ismail_*

*_CIGABAN - MATAKI NA BIYAR:- FICEWA_*
 
*_D- Yawan Samun Sabani Da Juna Fiye Da Rashinsa._*

      Idan ya zama mijin yana son ayi gabas matar ta je yamma, ko yana son yara su yi wani abu ita kuma ta ji ba ta son haka, ko kuma tana son ta ringa fita shi kuma yana qin haka to wannan alama ce ta samun sabani, kuma yin hakan na nuna alamar ficewa. Idan an tuna a mataki na farko, burin ma`aurata ne su yi abin da wanda suke Qauna yake so, to yayin da aka kai matakin cewa abin da yake so shi ne abin ki a wajen daya bangaren, to wannan an kai kishiyar wancan mataki na farko daga nan kuma an fice.
   Akwai alamu da yawa da za su iya nuna qaramin ficewa bayan wannan, amma wadannan su ne mafi bayyana a zamantakewar aure. Bayan qaramar ficewa akwai babbar ficewa, wanda take biyowa bayan qaramin, shi ne namiji ya saki matarsa, ko kuma ita ta meni khul`i, ko kuma ta bujure ta tafi gida ta ki dawowa. Abubuwan da suke taimakawa wajen kawowa ga wannan mataki suna da yawa, zamu kirgo mafi yawan aukuwa daga cikinsu:-

    *_a- Kwatantawa._*
          Ma`ana kwatantawa miji da wani, ko mutum ya kwatanta matarsa da wata, wannan kwatance ya hada da wajen kyau, ko wajen mu`amala, ko wajen asali, ko wajen dukiya, ko karatu. Allah Bai halicci mutane daidai wa daidai ba, wani ya fi wani, kuma wani bazai taba zama wani ba, amma kuma kowa yana da wani abu da wani bashi da shi, ko an sani ko wannan abun a boye yake. Saboda haka duk mai buqatar dawwamar aure, kada ya kuskura ya kwatanta nasa da na wani, domin wannan wani sababi ne na gaggauta ficewa daga masana`antar aure, da kuma sanya wa kai damuwa a kan abin da ba hakika ba ne.

   Manzon Allah ﷺ yana da mataye da dama, amma kowace daban take, Nana Khadija ba ta yi daidai da Nana Aisha ba, ko wacce tana da na ta abin da ta kebanta da shi. Nana Zainab ba daidai take da Nana Um-Salama ba, kowace tana da abin da takebanta da shi, kuma duk hudun ba su yi kama da juna ba, ballantana a kwatanta su, ko a nemi duk sai sun zama hoto iri daya. 

  *"b- Rashin Qarba._*
          Yayin da mace take son dole sai mijinta ya canja ya zama kamar wani da take tunani, ko shi yana tunanin dole sai ta zama kamar wance, to a wannan lokacin mutum zai tubure ya qi wannan Qoqarin. 
  Abin da yake lallai a kan mace ta karbi mijinta a yanda yake ta zauna da shi a bisa wannan fahimta da ta yi masa, shi ma ya yarda da ita a bisa yadda take ya zauna da ita a hakan.

  *_c- Rashin Gir'mama Juna._*
    Yayin da aka rasa qaddara juna tsakanin ma`aurata, ta han-yar jiz'ga juna, ko rashin ganin darajar juna, to wannan abu ne mai gaggauto da ficewa daga aure. 

  *_d- Rashin Sanya Juna Cikin Al`amura._* 
    Idan ya zamanto namiji yana gudanar da wani abin da ya shafe su baki daya amma ba ruwansa da shawara da ita, to wannan sababi ne na ita ma ta yi hakan kuma wannan zai gaggauto ficewa daga aure. Kamar haka ita ma ya ga tana shawara da wasu sannan ta ba shi labarin abin da za ta aikata, to a wannan yanayin zai fice ya bar mata aure. Idan wani abokin miji ko dan uwansa idan ya zama da shi ake shawarar, saboda tana kishin cewa wannan abu nata ne amma ya zo ya yi kaka-gida a ciki. Haka shi ma idan ya fahimci cewa tana da wasu kayanta ko abubuwanta wanda ba ta taba sanar da shi ba, sai dai ya ji a wani waje to wannan dalili ne na ya fice daga auren.

*_Zamuci gaba Insha Allah_*

*✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd*

Post a Comment (0)