YAREN SOYAYYA 14


*_💝🌹//YAREN SOYAYYA 014//🌹💝_*

 *_Mawallafi:- Dr Abdulkadir Ismail_*

 
     *e) Rashin Stayawa Akan Wani Abu da Aka Cimma da Juna.* 

     Idan ma`aurata sun cimma wata matsaya akan yin wani abu, ko qaurace wa wani abu, sannan wani ya saba, to wannan daliline da yake sanya ficewa. Idan tana yin wani abu ya hana kuma ta dauki al-qawarin ta daina ya kamata tana sake yi, to to wannan daliline da zai harzuka shi har ya fice. Idan ya yi mata al-qawarin sayo mata ko yi mata wani abu, amma daga baya ya ki, to shi ma wannan yana iya zama dalili wajenta na ficewa daga auren. 

    *f) Rashin Tankwaruwa.*

         Idan fahimtar ma`aurata ta zama; ko dai abu ya yi zama fari sal ko ya zama baqi qirin, to wannan sun rasa tankwaruwa. Abin nufi da tankwaruwa, shi mutum ya fahimci cewa idan abu ba fari ba ne sal, to watakila fari-fari ne, ko kuma ruwan kwaine, ko kuwa kore ne, amma ba ya nuna cewa lallai wannan abin ya zama baqi kuma wuluk. Kuma wani baqin ba wuluk ba ne, baki-baki ne, ko kuma ruwan qasa-qasa ne, ko kore mai duhu ko shudi mai duhu. Ma`ana idan abu bai samu yadda mutum yake so, to ya yi farin ciki cewa an samu, duk da bai cika cif da cif ba. Wannan kuwa *Manzon Allah ﷺ ya umarce mu da ``..Kintaci daidai, mu kusanta...``. [Bukhar: Hadisi na 39, 1/16].* Amma yin abu dari bisa dari wannan ba siffar dan Adam ba ce. Idan aka nemi cewa sai ya yi abu dari bisa dari, kuma idan ba haka aka yi ba bai yi daidai ba, to wannan sababi ne na ficewa daga aure.

   *g) Rashin Cimma Wani Abu Tare.* 

    Mutum a rayuwa yana son idan ya yi wata `yar tafiya, ya ga ya cimma wani abu a tafiyar da ya yi, shi ya sa a aure, mutum yakan so ya ga ya yi gaba a zamantakewarsu da iyali, idan ya rasa wannan sai ya fara tinanin ficewa. Wani yana son ya ga an cimma wata nasara a karatu, wani kuma tana sana`a tana dan samun wani abu ba cima-zaune ba ce. Rashin hakan na sanya korafi tsakanin juna, wanda wannan yake sawa a fice, za ta yi qorafin bai damu da yagama ginin saba, bai damu da ya gyara sana`arsa ba, bai damu da ya samar da wani tsari na karatun `ya`yansa ba. Wani lokacin a matakin kowanansu daidaiku, sannan kuma cimma burin yana kasancewa a matakinsu na gaba daya, haihuwa cimma wani abu ne, tarbiyyar yara ma haka. Shi ya sa a Musulunci ake son su yi sallar dare tare, su yi azumi tare, su zauna tare su tattauna da dai sauransu. Rashin cimma buri a rayuwa dalili ne daga cikin dalilan ficewa daga aure. 

  Wadanda dalilai ne na ficewa daga aure, duk da cewa ana ganinsu qananan dalilai, amma kuma suna da tasiri kwarai wajen ficewa daga aure. Wadanda suke biyo musu su ne manyan dalilai :-

  *a) Izgilanci.* 

     Yi wa juna ba`a da izgilanci a kan wata halitta ko shiga, wannan dalili ne mai qar'fi da yake gaggauta fita daga aure. Kamar ta yi masa izgilanci a kan sanqonsa misali, ko gurguntakarsa, ko wani abu na halittarsa, ko shi ya yi Mata izgilanci kan halittarta, ko wata shiga da ta yi, ko ya nuna wani abu nata ne ya sanya shi nesa da ita, kamar wurin jiki, ko wani abu makamancin haka.

*b) Wulakanci.* 

       Idan aka fara samun wulaqanci tsakanin ma'aurata, to wannan alama ce ta ficewa, wulaqancin na iya kasancewa a kan Mata ko mijin, ko kuma Iyayensa, ko `yan-uwansa. Wani lokaci a kan fahimci kamar wani daga ciki yana jure wulaqanci, amma haqiqanin al`amari shi ne, ya fice daga cikin aure, mai yiwuwa yana hangen wata maslaha ko wani dalili da zai hana shi ficewa bai daya.

*c) Rowa.* 

      Rowa iri biyu (2) ne a zamantakewa, ko dai ya zama rowar abin duniya wanda ake iya gani, ko kuma rowar Qauna da jin mutum a zuciya.... 

*_Zamu dakata anan_*


*_Insha Allah gobe zamu tashi daga wannan mataki na Rowa_*
 

*_Zamuci gaba Insha Allah_*

*✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd*
Post a Comment (0)