*💝🌹//YAREN SOYAYYA 012//🌹💝*
*_Mawallafi:- Dr Abdulkadir Ismail_*
*_MATAKI NA BIYAR:- FICEWA_*
Lura da abin da bangaren kyau a rayuwa yana janyo abu mai kyau, kira da baki ko da zuci na abubuwan da ba su day kyau sukan gaggauto zuwansu. *Manzon Allah ya ce:-*
*وَأُحِبُّ الْفَأْلَ الصَّالِحَ*
*_``Ina son kyakykyawar fata (zato, tunani)``._*
Idan mutum ya yi kyakykyawan fata sai abu ya zo masa irin yadda ya yi zato da Izinin Allah, idan kuwa ya yi mummunar fata sai abu ya zo masa irin yadda ya yi zato. A wannan mataki na ficewa ma`aurata suna gaggauto da halarto da tunanin mummunan abu, sai ya yi ta aukuwa irin yadda suka halarto da shi a zuciyarsu, ko suka furta da bakunansu.
Kafin isowar wannan mataki abubuwa ne suke tattaruwa daya bayan daya har su sana`anta matsalar da takan janyo ficewa. Saboda haka yana da muhimmanci a lissafo wadannan abubuwan da kuma irin gudunmawar da suke bayarwa wajen gaggauta ko dakile ficewar, aikata su na sanya daya bangaren ya ji cewa lokaci ya yi na ficewa, nisantarsu kuwa yana sanyawa a qauracewa ficewa ko a jinkirta lokacin.
Ficewa a zamantakewar aure kala biyu ne ; akwai qaramin ficewa, shi ne ma`aurata su fara jin cewa lallai ba ruwansu da juna, ko ba sa buqatar juna. Idan mutum ya sami kansa a cikin daya daga cikin wadannan alamomi to lallai ya kai qaramar kofar ficewa daga aure:-
*_A:- Ganin Juna Da Kuskure Da Yin Daidai Ba._*
Babu abu mai tada hankali a zamantakewa kamar haduwa da abokin zama ko abokiyar zama da kullum tinanin sa sai an yi abu daidai dari bisa dari 100%, irin wadannan ba wani abu da mutum zai yi su ga wannan daidai ne. Kullum abin da ya iya shi ne gano wani abu da aka yi ba daidai ba. Gano wani abu na ba daidai ba abu ne mai kyau. Amma duk lokacin da ya koma kuma dalili ne na munana fahimta a kan abokin zama to wannan ya zama matsala.
*_B- Ma`aurata Su Ringa Kokarai Kin Haduwa Da Juna Sai Da Kyar._*
Yayin da ma`aurata suke qoqarin kaucewa ganin juna a gida, ta yadda zai iya ficewa lokacin da take barci, ko ya dawo a makare bayan ta yi barci, ko kuma ita ta qi shigowa inda yake in ba shi ya je ba, ko ta kir-kiri fita unguwanni don ta yi nesa da shi, to a wannan lokacin ma`aurata sun fice daga cikin masana`antar aure. Wani lokacin qauracewar juna na faruwa ta han-yar qin yin magana da juna, ko kuma takaita magana a kan neman wani abu kawai ba tare da wata hira da take hada su ba, ko kuma qin neman juna yayin da ya yi tafiya ko qin yin saqon kar ta kwana. Yayin da mai aure ya fara jin cewa yafi jin dadin kasancewa da wasu fiye da abokin zamansa, to wannan alama ce ya fara ficewa daga masana`anta.
*_C- Qauracewa Haduwa Da Juna A Wajen Taro._*
Idan ma'aurata suka fara kyamar a gansu da juna a wajen taro ko wani waje na musamman, to wannan alama ce sun fara ficewa. Wani lokacin mace za ta ji ba ta son mijinta ya kaita unguwa gara ta tafi da wasu, ko ta yi tafiyarta ita kadai. Wani lokacin don kada a gan shi tare da ita zai iya neman uzuri na qin kaita unguwa ko halartar wani taro da za a gansu tare. Idan miji ko mata ba ta jin alfahari a ganta tare da mijinta a wani waje to wannan alama ce ta ficewa, domin kamar mutum yana son ya gamu da wani daban wanda ya fi abokin zamansa.
*_D- Yawan Samun Sabani Da Juna Fiye Da Rashinsa._*
*Insha Allah zamu tsaya anan sabida tsayin wannan Mataki... Insha Allah zamu tashi daganan a rubutun mu nagaba*
*_✍️ Ibrahim Muhammad Abu Muh'd_*