FALALAR KAUNA DON ALLAH
Al-Imamun Nasa’iy da Ibnu Hibban sun ruwaito daga Abu Huraira (Allah ya ƙara masa yarda) ya ce: “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: lallai (a cikin mutane) akwai wasu bayin Allah wadanda ba annabawa ba ne (amma) annabawa da shahidai suna burin su sami irin ladansu. Sai aka ce: su waye su ya Manzon Allah? A faɗa mana su don mu ƙaunace su. Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: wasu mutane ne waɗanda suka ƙaunaci junansu don hasken Allah ba tare da suna da ‘yan uwantaka ko danganta ba. Fuskokin su suna yin haske (ranar kiyama) akan minbari na haske. Ba sa shiga cikin tashin hankalin da sauran mutane suke shiga. Ba sa shiga cikin baƙin cikin da mutane ke shiga. Sannan sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya karanta fadin Allah (ku saurara! Lallai waliyyan Allah ba sa cikin tsoro kuma ba sa baƙin ciki)”.
Allah ya sa mu dace.