FASSARAR WAƘAR VACHAADAYYO SAAMI
• Waƙa - Vachaadayyo Saami
• Shiri - Bharat Ane Nenu
• Shekarar Fita - 2018
• Harshe - Telugu =Hausa
• Sauti - Devi Sri Prasad
• Rubutawa - Ramajogayya Sastry
• Rerawa - Kailash Kher
• Fassarawa - Jamilu Abdurrahman
• Musali thatha mudatamukam merisipoyene merisipoyene
Tamojin fuskar tsoho tana haske.
• Gudise paaka guddi deepam merisipoyene merisipoyene
Fitilar bukkar talaka ita ma na haske.
• Rachabanda pakkanunna ramulorigullo gantaaa rangaranga sambaranga mogene
Ƙaraurawar majami'ar Ubangiji Rama tana kaɗawa da murna.
• Vachaadayyo saami ningi sukkaltho godugetthindi bhoomi
Ichadayyo saami…kottha rekkalni molaketthinche haami |2|
Shugabanmu ya zo, ƙasa da kanta ta ta riƙe masa lemar taurari. Ya bamu tabbacin samun sabbin fuka-fukai wa rayuwarmu.
• Katthi sutthi palugu paara theeyandi mana kashtam sukkalu kunkum bottuga pettandi Kunkum bottuga pettandi
Ya ɗauki kayan aikin da muke aiki da shi ya share zufar wahalarmu kamar ɗigon kumkum a goshinsa.
• Annam bette panimutle mana devullu, mari aayudhala poojalu cheddham pattandi, mari aayudhala poojalu cheddham pattandi
Kayan aikin da ke taimaka mana wajen samun na kanmu sune ababen bautarmu. Mu yi addu'a a gare su.
• Ammoru kannu therisina nava raathiri…Innaalla simma seekati thellaare samayam kudiri
Abar bauta Kali ta buɗe idanuwanta a Navaratri, a wannan biki mai alamun nasara akwai alamun hasken da zai haskaka duhun da ya mamaye rayuwarmu.
| Vachaadayyo saami |
|Shugabanmu ya zo|
• O matti godalu chebuthaayi seema manushula kashtaalu
Waɗannan katangun da aka gina da ƙasa su za su bayyana matsalolin wannan wuri.
• Ye dhaari gathukulu chebuthaayi palle bathukula chitraalu
Waɗannan hanyoyin masu ramuka su za su bayyana rayuwar mutanen ƙauyen.
• Pandagosthe prathi okkari manasu,mari parugayyedi putti perigina palle vaipega
Idan ranar biki ta kewayo, zuciyar kowa sai ta fara gudu zuwa ga ƙauyen da ya girma.
• Assalaina panduga yepudante aa kanna thalli kanti neeru thudichina rojegaaa
Haƙikanin ranar biki ita ce ranar da aka share hawayen mahaifiya.
• O naadu kala kala veligina raayalori seemidi, wenadu velavela bothe praanamantha chinna bothundi
Wurin da a shekarun da suka gabata yake cike da yabanya, yanzu ya bushe... Hakan ne ya samu damuwa.
| Vachaadayyo saami |
|Shugabanmu ya zo|
• Hey chethi vrutthulu nooraru chevagaligina pani vaaru
Ƙwararrun ma'aikata a shirye suke su yi aiki.
• Chemata bottu thadilone thalukkumantadi prathi ooru
Kowane ƙauye yana sheƙi ne da zufar aiki tuƙuru.
• Yenda poddhuki veligipotharu, Ee andhagaallu vaana jalluku merisipotharu
Waɗannan kyawawan matasan suna walƙiya a cikin rana kuma suna sheƙi a ruwan sama.
• Evvadi kanna thakkuva puttaru veellandiri laage baaga bathike hakkulu unnollu
Waye yace an haife su ne a gidaje mafiya ƙasƙanci, su ma suna da haƙƙin samun kyakkywan gobe kamar kowa.
• Palletoollu pattukommalani otti jola paata paadakaa, thalladillu thala raathalaku saayamedho cheyalantaa
Kada ku ɓoye zancen cewa "ƙauyawa sune ƙashin bayan kowace al'umma" a cikin littafai da waƙoƙi kawai. Ku yi ƙoƙarin taimakawa 'yan ƙauyen wajen canja mummunar ƙaddararsu.
| Vachaadayyo saami |
|Shugabanmu ya zo|
©️✍🏻
Jamilu Abdurrahman
(Mr. Writer)
Haimanraees@gmail.com