Fassarar Waƙar Tum Se Hi
• Waƙa - Tum Se Hi
• Fim - Sadak 2
• Harshe - Hindi - Hausa
• Shekarar Fita - 2020
• Sauti - Ankit Tiwari
• Rubutawa - Shabbir Ahmed
• Kamfani - Sony Music
• Rerawa - Ankit Tiwari & Leena Bose
• Fassarawa - Jamilu Abdulrahman
• Do Dil Safar Mein Nikal Pade
Zukata biyu sun fara tafiya a tare.
• Jaana Kahaan Kyun Fikar Karein
Ba tare da damuwa da bigiren (da za su) ba.
• Kahaan Thikana Ho Raat Ka
A ina za mu kwanta in dare ya yi?
• Subah Kahaan Pe Basar Kare
Ina za mu je yayin da gari ya waye?
N• Khoya Khoya Dil Mera Kehta Hai
Ɓatacciyar zuciyata tana ta kai komo akan cewa.
• Haan... Tum Se Hi, Bas Tum Se Hi
Saboda ke ne kawai, saboda ke ne kawai.
• Meri Jaan Hai, Bas Tum Se Hi
Ina jina a raye ne, kawai saboda ke.
• Dil Ko Mere Aaraam Hai
Zuciyata na cikin kwanciyar hankali.
• Pareshaan Hai, Bas Tum Se Hi
Zuciyata kan damu ne, kawai saboda ke.
• Jo Dard Ko, Sukoon De
Wacce ke gamsar da raɗaɗina.
• Woh Dard Tum Se Milta Hai
Ke kaɗai ke bani irin wannan raɗaɗin.
• Aye Dil Zara Itna Bata Kyun Ishq Unse Hota Hai
Ya ke zuciyata, ki faɗa min me ya sa nake sonta?
• Saanson Ko Ab Jeene Ka Jaise Sahara Mile Gaya
Numfashina ya samu dalilin numfasuwa yanzu.
• Khoya Khoya Dil Mera Kehta Hai
Ɓatacciyar zuciyata tana ta kai komo akan cewa.
• Haan... Tum Se Hi, Bas Tum Se Hi
Saboda ke ne kawai, saboda ke ne kawai.
• Meri Jaan Hai, Bas Tum Se Hi
Ina jina a raye ne, kawai saboda ke.
• Dil Ko Mere Aaraam Hai
Zuciyata na cikin kwanciyar hankali.
• Pareshaan Hai, Bas Tum Se Hi
Zuciyata kan damu ne, kawai saboda ke.
• Aashiqui Hoti Hai Kya
Shin menene so?
• Dil Ko Mere Maloom Na Thha
Zuciyata ba ta san wannan ba.
• Ek Bhi Teri Tarah Chehra Koi Masoom Na Thha
(saboda) bata taɓa ganin fuska irin taki ba sai yanzu.
• Haan Yun Laga Iss Jaan Mein Ek Jaan Si Daakhil Hui
Ji na yi kamar wata rayuwa ce (ta daban) ta shiga jikina.
• Ab Toh Har Lamha Mujhse Kehta Hai...
Matuƙar (zuciya) ta ci gabada faɗa min hakan bayan kowane minti.
• Haan Haan... Tum Se Hi, Bas Tum Se Hi
Saboda kai ne kawai, saboda kai ne kawai.
• Meri Jaan Hai, Bas Tum Se Hi
Ina jina a raye ne, kawai saboda kai.
• Dil Ko Mere Aaraam Hai
Zuciyata na cikin kwanciyar hankali.
• Pareshaan Hai, Bas Tum Se Hi
Zuciyata kan damu ne, kawai saboda ke.
• Tum Se Hi... Woo....
Saboda ke ne kawai.
©️✍🏻
Jamilu Abdulrahaman
(Mr. Writer)
Haimanraees@gmail.com