Kaico!
Bissmillah da sunan ilahi
Wanda ya aiko ɗan Abdullahi
Zan yi batu da tambihi
Bani dama sarkina ilahi.
Mu yaran zamani yau
Ba mu magana ayau
Iyaye na ta fama
Mu kuma muna ta fankama.
Ba mu tsoron ɓaci na ransu
Ba mu yin ladabi garesu
Ba ma biyayya garesu
Amma in buƙata ta tashi mu je wurinsu.
Ra'ayinmu kawai muke bi
Ko mara kyau ne shi za mu bi
Ra'ayinsu ko ba mu bi
Ko da mai kyau ne ba mu bi.
A hakan muke so wai mu ci gaba
Alhali da uwarmu muke gaba
Mun ce mu ne za mu shige gaba
Wai shugabancin ya fi ƙarfin uba.
To ta yaya ma zamu haske?
Bayan albarkar mun make?
Mun aje uwarmu a gefe
Mun ɓoye ubanmu a shinge.
Kaico! Wannan lamari da gyara
Shi ya sa ma har na ɓara
Ku ka ji ni ina ta ƙara
Sai ka ce wanda sago ya sara.
To wallahi mu yi hankali
An ce duniya ɗamarar jangali
Dole sai an bi ta a hankali
Ko kuma mu faɗa baƙin hali.
Allah ka ƙara wa iyaye lafiya
Ka sa mu gama da su lafiya
Mu zamo masu ƙaunar tarbiya
Ga manyanmu mu zam masu biyayya.
Sarki ka shiryar da mu
Da abokai da ahalinmu
Da dukkan 'yan danginmu
Ka sa shiriya a zukatanmu.
©️✍🏻
Jamilu Abdulrahaman
(Mr. Writer)
Haimanraees@gmail.com
Ameen allah ya bamu ikon gyarawa
ReplyDeleteAmin, Jazakallah Khair
Delete