MANYAN FA'IDOJIN SADAKA GUDA 8


MANYAN FA'IDODIN SADAKA GUDA 8

*A-Na farko:*
Fa’idojin Sadakar Tadauwu’i Akan Mutum

*1-Tsarkake zuciya*
Allah Madaukakin Sarki ya ce,
*(Ka karbi sadaka daga dukiyoyinsu,ka tsarkake su ka gyara su da ita)*
@Attauba:103.

*2–Koyi ne da Shugabanmu Muhammad( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ )*

Saboda yana cikin halayensa kyauta da alheri,yana yin kyautar wanda ba ya tsoron talauci,yana cewa Bilal R.A:
*(Bilal ka ciyar,kada ka ji tsoron kadan daga wajen Ma’abocin Al’arshi (Allah) [Talauci])*
@Al-bazzar ne ya rawaito shi.

*3–Allah yana mayar da abin da aka ciyar, kuma wanda ya bayar ya qara samun Daukaka*

Allah yana cewa : *(Babu wani abin da zaku ciyar face sai Allah ya mayar da shi,shi ne mafi alherin masu azurtawa)* 
@Saba’i:39.

*4-Tsarkake dukiya ne daga haniyar ciniki*

An karbo daga Qais Dan Abi Garazata – Allah ya yarda da shi ya ce;“Mun kasance a zamanin Manzon Allah( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) ana kiranmu dillalai, sai Manzon Allah ya wuce ta wurinmu,ya sanya mana sunan da ya fi kyau, ya ce mana:
*(Ya taron attajirai,a cikin kasuwanci akwai yasassun maganganun da rantse-rantse,to ku gauraya shi da yin sadaka)*
@Abu Dawud ne ya rawaito shi.

*5-Samun lada da kankarewar zunubai*

Saboda fadin Manzon Allah( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ)
*(Wanda ya yi sadaka da kwatankwacin dabino na dukiyar halal – Allah ba ya karba abu sai mai tsarki – to Allah zai karbi wannan sadaka da hannun damansa, sannan ya rene ta ga mai ita,kamar yadda Dayanku yake renon dan dokinsa,har ta zama kamar dutse mai girma)*
@Bukhari Da Muslim ne suka rawaito shi.

*6-Ci gaba da amfanuwa da ladan sadaka mai gudana bayan mutuwa*

An kabo daga Abu Huraira–Allah ya yarda da shi – ya ce, *“Idan mutum ya mutu,ayyukansa sun yanke sai guda uku, sai sadaka mai gudana,ko ilimi da ake amfanuwa da shi,ko Da na gari da yake masa addu’a”* @Muslim ne ya rawaito shi.

*B-Na biyu:*
Fa’idodin Da Suka Shafi Al’umma Gabadaya
*7-Sadaka tana cika saqon da zakka take isarwa a cikin mutane.*

*8–Samar da hadin kai da taimakon juna da soyayyya a cikin al'ummar musulmi*

ALLAH NE MAFI SANI

*Allah ka bamu wadata da ikon yawaita Sadaka dan girman Hannayenka masu ciyarwa akowane lokaci.*
Post a Comment (0)