KHUƊUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE: 🌐29/JMD-AKHIR/1442-HJRY 🌐12/FEBRUARY/2021-MLDY



KHUƊUBAR MASJIDIS SALAFIYYA BIU BORNO STATE:
🌐29/JMD-AKHIR/1442-HJRY 
🌐12/FEBRUARY/2021-MLDY

🎙️GABATARWA👉🏼 Abubakar BN Mustafa Biu 

♦️TOPIC👉🏼 {FURFURA➖MAI GARGAƊI...} 

➖MUN KASASHI GIDA 5️⃣

1️⃣➖MUQADDIMA✔️
  Haƙiƙa mafi tsadar abu shine rayuwar mutum musulmi dukkansa musammanma lokacinda yakeda ƙarfinsa, tabbas rayuwarka gaba ɗayanta tun daga balaga abin bincikene da hisabi a lahira, 
💡ALLAH SW yace <<shin bamu rayar daku bane lokacinda yadace mai wa'azantuwa ya wa'azantu kuma MAI GARGAƊI yazo muku>> (SRT FAƊIR-36)

2️⃣➖WANENE MAI GARGAƊIN⁉️MAGANGANUN MALAMAI AKAI👉🏼
  Haƙiƙa Malamai sunyi saɓanin nau'i akan ma'anar <<MAI GARGAƊI yazo muku>>
👉🏼Wasu sukace (MUTUWA) 
👉🏼Wasu kuma (ANNABI SAW)
👉🏼Wasu kuma (QUR'ANI) 
👉🏼Wasu kuma (MUSULUNCI) 
👉🏼Wasu kuma (SHEKARU 18)
👉🏼Wasu kuma (BALAGA) 
👉🏼Wasu kuma (FURFURA) 
  Don haka idan Musulmi yaga ɗaya daga GARGAƊINNAN yazo masa wajibinsane yadage wurin ibada da neman yardan ALLAH SW,
◼️MAWAƘI yace👉🏼
  👉🏼bugun zuciyar mutum nace masa
   👉🏼lalle rayuwa daƙiƙaine da mintoci, 
   👉🏼kaɗaukaka anbato wa kanka kan mutuwa
   👉🏼anbato ga mutum rayuwace tabiyu
◼️SUFYANUL TSAURY yace= FURFURA shine MAI GARGAƊI, wanda gemunsa da kansa sukayi furfura to yayi tanadi ga ƙabari kuma yasayi likkafani‼️
◼MAWAƘI yace=
  👉🏼ribaci baƙin gashinka kafin yayi fari
  👉🏼dominfa duniya katangane ke gab da faɗuwa

3️⃣➖SUN CE AKAN FURFURA‼️
➖SAMARTA damane da duk wanda yasuɓuce masa yake kewarta, 
◼️Haƙiƙa Malamai da Salihai sunyi kuka sosai yayinda sukaga furfura tafito musu, domin shi tambarine (STAMP) na mutuwa, kuma mai korawane zuwaga ALLAH SW, 
◼️IMAM AHMAD yace= Wallahi babu abinda nake misalta samarta dashi- face kamar wani abune yakasance a hannuna sai kuma yafaɗi daga hannun nawa, 
◼️ABUL ATAHIYYAH yace👉🏼
  👉🏼nayi kuka da hawayen idanuna akan shuɗewar samarta amma kukan batayi anfaniba
  👉🏼inama da samartan zai komo wata rana in bashi labarin abinda tsufa ta mini
  👉🏼Wato ta canza mini launi da haske da kamanni, ta ruguza ƙarfina da zaƙin muryar waƙata, ta lanƙwasa bayana, ta sani kuka ta hanani barci, 
◼️WARAQAH IBN NAUFAL R/A yacewa ANNABI SAW= kaico! inama da inada ƙarfin ƙuruciya da na ƙarfafeka, 
◼️Matasane suka kwana a ɗaki ɗaya da wani dattijo, nishinsa da gurnaninsa da rashin barcinsa ya hanasu barci har asuba, bayan sunyi sallar asubahin sai sukace masa= ka hanamu barci, sai yace= kuyi haƙuri, tamaninne yasani, wato na tsufa nakai shekaru 80,

4️⃣➖YI HAƘURI KAIMA ZASU BAKA IRINTA‼️
◼️IBN QUTAIBAH yace= wani dattijo tsukuf daga BANY GIFFAR mai farin gemu mai tsawo yazo wucewa kusada wasu matasa suna wasa sai ɗayansu yace dashi= nawane kasayi wannan bakan🏹? wato yana izgili da furfuran, Sai idanun dattijon yacika da ƙwalla sai yace= ya ɗana, wannan farin gemun shekarune suka banisu kyauta, KAIMA ZASU BAKA IRINTA‼️

5️⃣➖RUFEWA🔒
  Yadace ga mutane musammanma matasa suriƙa girmama dattijan cikinsu, 
◼️IMAM AHMAD- ance baya tashiwa don marabtar wani koda Sarkine ko Mai kuɗi ko mai matsayi, amma in yaga dattijo mai farin gemu zai taso yarungumeshi yasunbaceshi yazaunar dashi kusa dashi, 
◼️IMAM ZAHABY- ya ambato cikin tarjamar (YAHYA IBN UKTSUM) cewa shi alƙaline wanda Sarki MA'AMUN yanaɗashi saidai ba'aji daɗin siyasar salon alƙalancinsaba, bayan mutuwarshi an ganshi a mafarki akace dashi= yaya ALLAH yayi dakai⁉️ Sai yace= Na rantse da wanda raina ke hannunsa- ALLAH SW yazaunar dani agabansa sai yace dani <<na rantse da izzata- da badon furfurarkaba da na azabtar dakai da wuta>> sa'annan sai yashigar dani ALJANNAH, 
  Yaku bayin ALLAH! wannanfa ba lasisi aka bawa Tsoffi su aikata abinda sukeso bafa tunda ALLAH yana kunyar furfurarsu, ma'anarsa ALLAH yana kunyar mai kunyarsa, shiyasama👉🏼
💡ANNABI SAW yace "mutune uku ALLAH bazai kallesu ranar ƙiyamaba kuma bazai tsarkakesuba sunada azaba mai raɗaɗi" daga cikin ukun yace "da tsoho mazinaci"

👏🏻YA ALLAH KABAMU ƘURUCIYA MAI KYAU👏🏻 TSUFA MAI KYAU👏🏻MUTUWA MAI KYAU👏🏻MAKOMA MAI KYAU👏🏻
AMIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIIN👏🏻👏🏻👏🏻

via👉🏼Abubakar BN Mustafa Biu✍️
Post a Comment (0)