TASKAR TARIHI 25

*TASKAR TARIHI [25]*

 ```🖍 AUREN MANZON ALLAH (SAW) DA KHADIJATUL KUBRAH (RA)``` 

Ita Khadija ƴar Khuwailid (RA) ta kasance Mace ce wadda take da gaske take yin al’amarin ta, sannan Mace ce mai Daraja, daga cikin mafi ɗaukakar Nasaba da Dangantaka daga cikin Ƙuraishawa, kuma ta kasance daga cikin Matan da suka fi kowa yawan Dukiya, don Ayarinta yakan zama kamar Karafkar Ƙuraishawa gaba-ɗaya, takan ɗauki Mazaje haya, sai ta ɗauki Dukiya ta basu suje suyi Kasuwanci, da sharaɗin abunda suka samo za’a basu kaza, sakamakon wannan hidima da suke mata ta Kasuwanci, su kuma Ƙuraishawa dama ƴan Kasuwa ne.
 
Yayin da labarin Gaskiyar Manzon Allah (SAW) ya isa gareta na in ya faɗa yana cikawa, da kuma girman Amanar Shi, da kuma irin manya-manyan Ɗabi’u na mutunci waɗanda yake dasu, sai tayi sha’awar ya ɗauki dukiyar ta ya fita da ita zuwa Ƙasar Sham yaje yayi kasuwanci da wannan Dukiya, tayi ma Annabi alƙawarin baShi ninki biyun abunda ta saba ba Mazajen da suke mata Kasuwanci, sai Manzon Allah (SAW) Ya karɓi wannan buƙata tata, Manzon Allah ya fita wannan Kasuwanci tareda wani Yaron Khadijah mai suna “Maisarah”.
 
Hakika wannan Yaro na Khadijah mai suna “Maisarah” a wannan tafiya da sukayi tare da Annabi SAW yaga ayoyi masu ɗimbin yawa, sannan kuma yaga irin Ɗabi’u na Manzon Allah SAW, sannan yaga irin gaskiyar amanar Annabi SAW wajen Kasuwanci, da Baiwa iri-iri wadda Allah Yayi wa Annabi da kuma abubuwan ban mamaki da suka faru ga Annabi. 
 
Bayan sun dawo daga wannan Kasuwanci ne, sai Maisarah ya kwashe labari gaba-ɗaya ya baiwa Uwar gidan shi Khadijah. Manzon Allah Ya dawo mata da Riba sai taga ribar ta ninka ninki biyu na abunda ake samo mata, ita ma sai ta ninka miShi abunda tayi alkawarin baShi. 

Da Khadijah taji irin waɗannan Labarai masu ban sha’awa daga Yaronta gameda Manzon Allah SAW, wannan labarin da Maisarah ya gaya mata sai ya ƙara ƙarfafa mata abubuwan da taji dama kafin a fita wannan Kasuwancin, daman Khadijah Mace ce wacce al’amuranta da gaske take yi, Mace ce mai kaifin Basira, amma da Allah Ya tashi nufan ta da alherai da girmamawa sai ya haɗa ta da Annabi SAW, a wannan lokacin Khadijah tafi duk Matan Ƙuraishawa girman daraja, ta fisu ɗaukaka, kuma duk tafi su Kuɗi da Dukiya. 
 
Duk Mazajen Ƙuraishawa suna kwaɗayin su Aure ta, duk Namijin da zai samu iko akanta so yake ya Aure ta, amma a haka sai ta gabatar da kanta ga Annabi SAW, tace: “nifa ina Sha’awar Auren ka, saboda dagantakar ka dani kuma naga kana da girman daraja da Amana da kuma kyawawan ɗabi’u”. Sai Annabi SAW yaje Ya faɗa wa Baffanin shi wannan magana, akaje aka samu Baffan Khadijah mai suna Amru ɗan Asad akayi maganar Aure.
  
Manzon Allah Ya Auri Khadijah ne a Shekara ta 25 da rayuwar Shi, ita kuma tana da Shekara 40. Kafin wannan Aure da Khadijah tayi da Annabi SAW ta taɓa Aure sau biyu.

✍ *ANNASIHA TV*

*Twitter* 👇
https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09

*Telegram* 👇🏽
https://t.me/AnnasihaTvChannel/5460

*WhatsApp* 👇🏼
https://wa.me/2348142286718?text=Assalamu%20Alaikum%20Zan%20So%20Na%20rika%20samun%20aiyukan%20AnnasihaTv.%0A%0


Post a Comment (0)