SHARHIN FIM ƊIN TOILET EK PREM KATHA


SHARHIN FINA-FINAI 

Shiri ne da yake zuwa duk ranar Litinin wanda ake zaƙulo fina-finan India ɗaya bayan ɗaya ana sharhi ko tattaunawa akai, a wannan zaure ƙanƙashin jagorancin

Abba India Dala
Auwal Ibrahim KJ
Adam DG Auta

A wannan makon muna tafe ne da ƙasaitaccen shirin nan na jarumi AKSHAY KUMAR da BHUMI PEDNEKAR mai suna "TOILET EK PREM KATHA".

                         GABATARWA

"TOILET : EK PREM KATHA" fim ne mai ɗauke da salon barkwanci da ya fita a shekarar 2017. Shree Narayan Singh ne ya bayar da umarni, Akshay Kumar da Neeraj Pandey suka shirya shi. Yayin Akshay Kumar da Bhumi Pednekar suka jagorance shi, Anupam Kher, Sudhir Pandey da Divyenda Sharma suka taimaka musu.
     Fim ne na ban dariya dake tallafawa wajen yaɗa manufofin gwamnati kan inganta yanayin tsafta a India tare da ƙarfafawa wajen kawar da yin amfani da sararin fili dan biyan buƙatar bayan gida (Toilet) musamman a yankunan karkara.

                   LABARIN FIM ƊIN 

A wani ƙauye na India, wasu ayarin mata ne suka nufi wani fili dake can wajen ƙauyensu kusa da Gorakhpur da sanyin safiya domin biyan buƙatar bayan gida (wanka etc).
     Daga ɗaya gefen jarumin ciki mai suna Keshav wanda mahaifinsa ya kasance mai tsananin riƙo da addini da kuma canfe - canfe ya haɗu da wata budurwa Jaya ta kasance mai ilimi ya kamu da sonta har ya shawo kanta kan ta aure shi. Amma shi mahaifin nasa yana ganin cewa taurarin Keshav sun nuna cewa mace mai babban yatsa biyu a hannun hagu kawai zai aure goben sa tayi kyau. Tunda Jaya bata dashi sai Keshav yasa aka yi na bogi ya bawa Jaya ta saka kamar zobe a yatsanta. Ba tare da zargin komai ba mahaifin nasa ya amince da auren.
     A safiyar farko da tayi a gidan Keshav, Jaya ta fita can bayan gari domin biyan buƙatar bayan gida ba dan taso hakan ba, amma sai ta dawo gida cikin ɓacin rai ba tare da tayi abinda ya kaita ba tana mai yiwa Keshav ƙorafi. Duk irin ƙoƙarin da zai yi domin yaga ya fahimtar da ita akan ta janye maganarta ta lallai a gina bayan gida yayi amma taƙi yarda. Sai ya samar da wata mafita ta wucin gadi dan magance matsalar a inda da farko ya ɗauke ta zuwa ga maƙota wanda suke da bayan gida, sai kuma daga baya yake kaita cikin jirgin ƙasa da yake tsayawa a tashar jirgin tsawon mintuna 7 a ƙauyen, ba tare daya gina bayan gidan a gidansa ba, bayan wani lokaci, wata rana sai aka kulle ta a bayan gidan na cikin girji, shi kuma jirgin yabar tashar, cikin tunzura da damuwa Jaya tabar Keshav ta koma gidan iyayen ta.
     Bayan gazawa da yayi wajen shawo kan mutanen ƙauyen game gina bayan gida, sai Keshav tare da taimakon Jaya suka tuntuɓi hukumar da abin ya shafa sannan aka fara ginin a gaban gidan sa. A lokacin da aka kammala sai mahaifin Keshav suka shirya rushe ginin a yayin da shi kuma Keshav ke ta sharar bacci abinsa. Kafin su kai ga ida rushewa sai Keshav ya farka daga baccin yayi maza ya hana su ƙarasawar.
     Jaya ta shigar da ƙarar neman saki a kotu, ta bayar da dalilin cewa rashin bayan gida a gidan mijin nata ne yasa take so a raba su. Saboda yanayin case ɗin daya zo da wani sabon salo ya janyo hankalin kafafen yaɗa labarai. Nan 'yan siyasa da da hukumomin gwamnati da abin ya shafa suka ɗauki matakin gina bayan gida a ƙauyen su Keshav. Amma mahaifin nasa ya tsaya ƙememe kan ra' ayinsa na baza a gina bayan gidan a gidansa ba, har saida wata rana mahaifiyarsa tazo fita dan biyan buƙatar bayan gida ta faɗi har taji ciwo a kwankwason ta nan tayi ta kuka saboda baza ta iya takawa domin zuwa inda ta nufa ba dan haka ya zama dole tayi amfani da bayan gidan da Keshav ya gina a gaban gidan. Bayan tirjiya da aka sha, sai mahaifin Keshav ya haƙura ya taimakawa mahaifiyar tasa zuwa bayan gidan. Anan ya fahimci cewa bayan gida nada matuƙar muhimmanci a kowane gida.
     A ranar da za a saurari shari'ar su Keshav da Jaya, sai saƙo yazo wa alƙalin daga ofishin "Chief Minister" kan cewa kada ya raba su saboda a washe garin ranar za a fara gina bayan gari a gaba ɗaya ƙauyen. Nan ma'auratan suka fito cikin farin ciki. Mahaifin Keshav ya bawa Jaya haƙuri akan taurin kan daya nuna. Daga ƙarshe nan mutanen ƙauyen suka fara amfani da bayan gida na wucin gadi yayin da ake ci gaba da ginin a gaba ɗaya ƙauyen.

                               SHARHI 

Fim ne da aka sami nasara sosai a yadda Box Office India suka fitar cewa yakai matsayin super hit a kasuwancinsa. Fim ɗin yana nuni ne game da matsalar bayan gida na India, sakamakon banbance - banbancen al'adu da addinansu ya janyo hakan. Saboda wasu basu yarda da samuwar bayan gida a zaman takewarsu ba. A yankunan karkara dake India mutane har yanzu basu da wannan abin buƙata daya zama dole wanda hakan ke ɓatawa mata rai kuma hakan ke janyowa ana cin zarafin mata.
     Fim ɗin ya isar da saƙon da ake so a isar wanda hakan yasa ya sami shiga cikin nomination na best film ta Filmfare Awards, haka ma director Shree Narayan Singh shima ya sami shiga nomination. A saboda ƙoƙarin da jarumi Akshay yayi a fim ɗin shima ya sami wannan dama ta shiga cikin nomination na best actor ta Filmfare Awards.

                         TAURARIN SHIRIN

Akshay Kumar - Keshav Sharma
Bhumi Pednekar - Jaya
Divyendu Sharma - Narayan (Naru) Sharma
Anupam Kher - Dinanath (DJ Kakka) Joshi
Sudhir Pandey - Vimalnath Sharma (Mahaifin Keshav)
Atul Srivastava - Mr Jagdish Joshi (mahaifin Jaya)
Ayesha Raza Mishra - vidya Joshi (mahaifiyar Jaya)
Rajesh Sharma - Mathur
Shubha Khote - Rampyari (Kakar Keshav)

                         WAƘOƘIN CIKI 

1. Hans Mat Pagli
2. Bakheda
3. Gori Tu Latth Maar
4. Subah Ki Train
5. Toilet Ka Jugaad

           Sai kuma idan Allah ya nufe mu da ganin sati mai zuwa domin kawo wani fim ɗin.

             AUWAL IBRAHIM KJ (AIMAR)
Post a Comment (0)