#SUNNONIN DA AKA MANTA DA SU
*_A-Addu'a lokacin saukowar iska_*
Daga Nana A'isha رضي الله عنها,tana cewa:
"Manzon Allah ﷺ ya kasance idan Iska ya taso yana cewa;-
*(اللهم إني أسألك خيرها،وخير ما فيها،وخير ما أُرسلت به، وأعوذ بك من شرها،وشر ما فيها،وشر ما أُرسلت به)*
@رواه مسلم.
B-Sadar da dan uwanka wanda kake so,ka fada masa kana sonsa.
Daga Muqaddamu bn Ma'ady kariba رضي الله عنه,Lallai Manzon Allah ﷺ قال yace;
*(Idan dayanku yana son dan uwansa,to ya sanar da shi cewa kana sonsa)*
@رواه أحمد،وحسنه الألباني
C-Kurkurar baki bayan shan nono.
Daga Ibn Abbas رضي الله عنه,Lallai Manzon Allah ﷺ ya sha nono,sai ya kurkure bakinsa,kuma yace:
*(Lallai nono yana da maski da maiqo)*
@متفق عليه)
D-Yiwa dan uwanka Addua a bayan idonsa,kuma ba tare da saninsa ba.
Daga Abid dardaar رضي الله عنه,yana cewa lallai naji Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Duk wanda yayiwa dan uwansa addua batare da saninsa ba kuma a bayan idonsa,sai Mala'ikan da ake tara dashi ya Amīn,kaima Kana da irin abinda ka roqa masa)*
@رواه مسلم.
E-Zama a masallaci bayan sallar Assuba kana ambaton Allah har rana ta fito.
Daga Jabir bn Sumrata رضي الله عنه yana cewa,lallai Manzon Allah ﷺ ya kasance idan yayi Sallar Assuba,yana zama a wajan da yayi sallah,har sai rana ta fito ta danyi haske)*
@رواه مسلم.
C-Yin addua lokacin da kaji charar zakara da kuma neman tsari alokacin da akaji kukan jaki.
Daga Abi Hurairata رضي الله عنه,Lallai Manzon Allah ﷺ yace:
*(Idan kunji charar zakara,to ku roki Allah daga falalarsa,domin yaga Mala'ikane,idan kuma kunji kuka jaki,ku nemi tsarin Allah domin yaga Shaidhan ne)*
@متفق عليه.
Allah ne mafi sani.
*Karatun Hadisi da aiki da shine Zaman Lafiyar Musulmai*.