*TASKAR TARIHI [24]*
```📍Ɓangaren maganar Annabi gameda Yarjejeniyar Komai da ruwanka inda yace: ❝wannan Yarjejeniyar tafi mun daɗi da soyuwa a Zuciya ta fiye da in samu Jajayen Raƙuma, da za’a kiraye ne zuwa ga irin wannan aiki na alheri a Musulunci dana amsa``` ❞.
1⃣ Lallai Musulmi Adili ne mai tsaida Gaskiya ne koda tareda abokin husumar shi ne mas'ala ta kama, ka dubi Annabi Muhammad SAW yazo ne don ya tunkari wannan Jahiliyyah da tayi katutu a Ƙasar Larabawa, amma bai mata Adawa da Ƙiyayya a dunƙule da kuma a ɗeɗewarta ba (ba komai ne nasu ya yaƙa ba), har hakan yasa yazo yana musun abubuwan Alheri dake cikinta ba, a'a sai dai ma duk wani aikin alheri dake ga ita ya yabe shi ne, kuma Annabi yayi furuci da Daraja ga masu ita, koda kuwa sun kasance abokan husumar shi ne, kai koda ma sun kasance suna bayyana ƙiyayya da yaƙar shi ƙarara, kaji dai Annabi SAW yana yabon irin wannan Yarjejeniya.
Annabi yayi mana haka ne don ya nuna mana mu kasance masu adalci tareda abokan husumar mu, sannan kuma gaskiyar dake tare da waɗansun mu mu karɓe ta, kada Adawa ta tunkuɗa mu muƙi fahimtar alherin dake tattare da abokan husumar mu❗️.
Shi Manzon Allah SAW cewa ma yake yi: ❝Ni an aiko ni ne don in cika Kyawawan Ɗabi'u❞, anan Annabi yana ce mana: a Jahiliyya akwai kyawawan ɗabi’u, Shi yazo ne don ya cika su, kuma don ya ƙarasa su, Manzon Allah bai yi inkarin ɗabi'u kyawawa waɗanda suke dasu ba, saboda kaɗai sun nuna mishi ƙiyayya kuma sun yaƙe shi; don haka ake Nasiha ga Musulmi ya zama Adili, mutumin kirki, mai faɗin gaskiya tare da wanda yake husuma dashi.
Shi dai Adalci da tsayawa gaskiya, abun nema ne wanda wasu daga cikin Mutane sun gafala a wajen mu'amalar su tare da waɗanda suka saɓa musu, abunda yakai suke gafala suyi ƙememe basa iya faɗan wani alheri dake tattare da abokin adawar su, ko kuma duk wani saɓani dake tsakanin su.
Wannan kuma baya nufin baza'a ambaci kuskuren Mutum ba don tsoratarwa, ba haka ake nufi ba, babu makawa dole a bayyana kuskuren mutum, saboda tsoratarwa daga wannan kuskure, don kada wanin shi ya afka cikin wannan kuskure, sai dai ma wannan na daga cikin Babin umarnin da kyakkyawa da hani daga mugun abu da yake faruwa.
2⃣ Al'amarin da zamu sake fahimta anan, shi dai Musulmi mai kira ne zuwa ga alheri, don haka yana taimakawa duk wani wanda yake kira zuwa ga alheri, domin asalin shi Musulmi shi yafi dacewa da alheri, duk wanda yayi kira zuwa ga wani alheri ga zamantakewar Al'ummah; to Musulmi ya kamata ya zama mai taimako gareshi.
Ya kai Musulmi! Idan kaga wani yana kira zuwa ga wani alheri da za'a kawowa zamantakewa ko Gari na Musulmi, ko kuma wannan abun zai amfani Al'ummar Musulmi, ka zama farkon wanda zai taimakawa wannan da zai yi alherin ka zama kuma mai ƙarfafar guiwa, kar kazo kana Sharri.
Ita Da'awah ta Musulunci, tazo ne don ta karantar da Musulmi su zama masu tausasawa da kyautatawa tare da duk wani wanda ya tayar da wani alheri, kada wannan mai Da’awa na Musulunci ya taƙaitu da cewa sai abunda shi ya fara shine alheri, don haka duk abunda bashi ya fara ba, ba alheri bane❗️.
📝 ANNASIHA TV