AUREN SHA'AWA KO AUREN ALLAH DA ANNABI?

*AUREN SHA'AWA KO AUREN ALLAH DA ANNABI???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*MAJALIS - SUNNAH*
.
.
مجلس السنة
📓📔
+2349032091131
+237665087032
.
.
Yau 24/ 12/ 1441 wanda yayi dai-dai da 14/ 09/ 2020.
=
=
_Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyuakanmu. Hakika Wanda Allah ya shiryar Babu Mai 6atar dashi, Wanda ya 6atar Kuma Babu mai shiryar dashi. Kuma Ina Shaidawa babu abinda bautawa da Gaskiya sai Allah shi kadai, kuma ba shi da abokin tarayya. Kuma Ina Shaidawa Muhammad bawansa ne Kuma Manzonsa ne._

_Bayan haka, jama'a ba tareda 6ata lokaci ba zamu shiga bayanin mu a gurguje, wanda nake fatan yan uwan da muke tare dasu a wannan zauren musamman wadanda suke bibiyarmu akoda yaushe su nutsu su karanci wannan bayanan namu da kyau, sannan sanin kanku ne cewa bayan mun gama bayanin namu gaba daya a yau, tho kuna iya turoda tambaya akan abinda ya shafi wannan bayanin insha Allah ta'ala._

_Jama'a mu musulmai mun yarda da kadaitakar Allah s.w.t mun yarda cewa Allah shine abinda ya cancanta a bauta masa shi kadai babu abokin tarayya acikin bautar, kuma mun yarda cewa Annabi Muhammad Manzon Allah ne kuma bawansa ne, kuma mun yarda cewa abinda Allah s.w.t ya aiko Annabi Muhammad s.a.w na Alqur'ani da Sunnah, an aiko shi ne domin ya shiryar damu zuwaga tafarki mafi dacewa acikin rayuwarmu._

_Tho wanda duk ya yarda da haka kuma ya tafi akan wannan tsarin na Alqur'ani da Sunnah, tho zai rabauta duniya da lahira. Wanda kuwa ya kauce ma wannan tsarin, tho zaiyi asara duniya da lahira._

_Saboda haka dolene ka yarda cewa Allah s.w.t shi ya halicceka kuma shi kadai zai baka tsari akan yaya zakayi rayuwarka, domin babu dama kace wanda ya halicceka daban, wanda kuma zai baka tsarin yaya zakayi rayuwarka daban. Jama'a kuna fahimta??_

_Jama'a a tsarin Allah, abinda ake nufi da tsarin Allah shine *SUNNAR ALLAH*, kuma sanin kanku ne cewa Sunnar Allah baya canzawa haka Allah ya tsara. Idan Allah ya tashi zai shirya wani abu wa bayi, tho yana shirya abinda ya dace daku ne, ba wai yana shirya muku abinda kukeso bane. Jama'a kun fahimta?? Idan Allah ya tashi zai shirya maka wani abu, tho bazai kalli me kakeso ko meye bakaso ya shirya maka abun ba, amma zai dubi meye dace da kai meye dace daku, sai ya shirya muku alkhairanku akansa, ba wai yana kallo me kuke so ko meye bakwa so ya shirya muku ba._

_Shiyasa jama'a babu wanda zai wahala a rayuwar duniya da lahira kamar wanda ya dauki son zuciyarsa da ita zai rayu._

_Saboda haka jama'a duk abinda zamu karanta akan abinda ya shafi neman aure, ko wa za a nema, ko makomar zamantakewar auratayya, tho kada ka dinga tunani da kai abinda kaga ya dace, a'a ka bari ka dauki shawarar Annabi Muhammad s.a.w. Kada ka yarda kayi amfani da tunaninka ko kayi amfani da tunanin waninka, a'a kayi amfani da shawarar da shari'a tazo maka dashi domin duk abinda zai zamo maka alkhairi a rayuwa Allah ya kan kara maka abinda ya dace da kai ne, ba wai yana kallon me kakeso sannan ya kara maka abu ba. Jama'a kun fahimta??_

_Jama'a idan kun fahimta da kyau zakugane duk wanda kaga baya bin shari'a duk wanda kaga addini bai dameshi ba duk wanda kaga tsarin Allah bai dameshi ba wajan gudanar da al'amuransa, tho wannan sirrin ne bai gane ba (wato wannan ga66an da muke magana akai) ne bai ganeba. Jama'a kun fahimta???_

_Tho jama'a rashin gane ga66ar da mukayi magana akanta ne yasa yan uwanmu musulmai suke aure don sha'awa ba don abinda shari'a tace ba._ 

_Ita dai sha'awa itace abinda rai yakeso, ita kuma shari'a bata gina aure akan abinda mutum yakeso ba kamar yadda na fada a baya cewa Allah baya kara maka abinda kakeso sai abinda yaga ya dace da kai ne._ 

_Rashin sanin wannan ne yasa wani yake auren mace dan kyaun fuskar da take dashi, jama'a lalacewa ta kai lalacewa a Nigeria kaga hatta saboda hancin mace ake aurenta. Akwai wani bawan Allahn da muke hira dashi anan kasuwar wafa yake cemin shifah babban abinda ya jawo hankalinsa har ya auri matarsa shine hancinta kawai. Jama'a banda rashin sanin muhimmancin aure yaushe namiji zai auri mace saboda hanci kawai, me hanci zatayi masa jama'a?_

_Kunga duk irin wadannan abubuwan shirme ne, kuma ire-iren wadannan shirmen ne yake jawo matsalolin a zamantakewar aure. Wani kuma zai auri mace saboda kudinta, tho ire-iren wadannan dai shine abinda ake kira da auren sha'awa, kuma sanin kanmu ne cewa Annabi s.a.w yace mana: *"NA HOREKU DA MA'ABOCIYAR ADDINI* tho jama'a wannan addinin fah shine manufar da Allah da Manzonsa suka umarci bayi da suyi aure. Jama'a kun fahimta??_

_Saboda haka yakamata kusani cewa abinda Allah ya shar'anta muku yayin da zaku nemi aure, ko yayin da za ayi daurin aure, ko yadda zakuyi rayuwar aurenku, tho alkhairi ne a gareku. Rashin sanin wannan ne yasa yan uwanmu musulmai basa gina soyayyar su akan yadda shari'a ta shar'anta musu, wasu kuma sun sani amma saboda son zuciya bazasu dauki wannan tsarin na addini suyi amfani dashi ba yayin da zasuyi aure ko yayin da zasu nemi aure, tho amma kusani cewa duk wanda ya bi son zuciyarsa yayin da yake neman aure ko yayin da zaiyi aure, tho na rantse da Allah daga ranar ya shiga wahalar duniya da lahira._

_Jama'a na rantse da Allah wadannan mutanen nan da kuke ganin suna bukukuwa iri-iri da sunan wayewa da burgewa ko, tho basa samu zaman lafiya a zamantakewar su, kuma irinsu wallahi karshen zaman auratayyarsu bata yin kyau wallahi. Domin wallahi babu yadda zakayi ka bar tsarin Allah tsarin da Annabi Muhammad s.a.w yazo dashi ka kama tsarin makiyin addini kuma kuce zaku zauna lafiya. Wallahi bazai yiwu ba. Kuma ire-iren wadannan 6arnar da ake aiwatarwa a wajan bukukuwa laifin magabatan ne, kuma na rantse da Allah, Allah bazai kyaleku ba muddin baku tuba ba, domin da ace kun dauki hukunci yayin da zaku bada 'ya'yanku cewa baku yarda a shirya reception ba, baki yarda ayi taro wanda za a cakudu maza da mata har ma ku ma iyayen ku shiga cikin taron kuna tika rawa a gaban jama'a ba kunya ba tsoron Allah. Wallahi bakuci banza ba muddin baku tuba ba. Saboda haka wajibine a gareku iyaye yayin da zaku bada 'ya'yanku cewa baku yarda ayi shirmen da ake gabatarwa yayin da ake bukukuwa a yanzu ba, a'a abinda ku kukeso shine abinda Allah ya shar'anta. Jama'a kuna fahimta???_

_Saboda haka jama'a kuji tsoron Allah ku guji auren sha'awa, duk sadda kuka tashi neman aure tho ka fara duba nagartar wacce zaka aura ba kyaunta ba, saboda hakki ne akanka ka nemawa 'ya'yanka uwa tagari, na rantse da Allah idan ka bari ka dauko yar duniya ta zamo uwar 'ya'yanka ko, tho Allah zai saka musu, kuma Allah bazai kyaleka ba._ 

_Hakama kema kiji tsoron Allah idan zaki za6a miji, tho ki dubi nagartarsa ba wai ki dubi abin duniyar da ya tara ba, kema hakki ne akanki ki za6awa ya'yanki uba na gari, na rantse da Allah idan kika kuskura kika za6owa ya'yanki dan iska mutumin banza, tho wallahi Allah bazai kyaleki ba, kuma Allah zai sakamusu. Saboda haka ku bi shawarar da Annabi Muhammad ya bayar yayin da zaku za6i abokin zama ko abokiyar zama._

_Jama'a wallahi rashin kula da shawarar da shari'a ta bayar yayin da za a nemi aure ko yayin da za ayi auren yasa ma'aurata suke kuka, mata suke kuka cewa mijinsu yayi musu kaza da kaza. Kaga mace ta rubuto tambaya cewa mijinta baya wanka kuma tayi tayi yayi amma sai ya qi yi, tho ba dole ba jama'a, ko kuma kuji mace ta turoda tambaya cewa mijinta baya sakar mata fuska alhalin ita tana nuna masa soyayya, ai wannan ma mai sauki ne wallahi, karshen iskancin namiji shine ya kawo budurwarsa ko karuwarsa har cikin gidanki suyi iskancin da suka ga dama. Akwai yadda zakiyi?? Wallahi babu sai dai kiyita kuka ko kuma idan kinada karfi ki shekeshi ko makamancin haka, bayan nan akwai abinda kuke iyawa ne?? Tho ire-iren wadannan abubuwan da yake faruwa a zamantakewar aure shine rashin bin tsarin da shari'a ta bayar._

_Ba ana fadamuku cewa ku za6i nagartar namiji kuna ganin cewa rashin wayewa ne ba, tho Allah ya baki sa'a ki kuskura ki auri wani saboda abun duniyar da ya tara. Wallahi mata ku cire son duniya a zuciyoyinku, yawancinku yan mata bakuda wayo wallahi, in banda rashin wayo meye hadaki da mota har ma zaki iya auri wani saboda mota? Motar da idan ya aureki tho da wahala ya dinga daukarki ya kaiki unguwa. Wallahi mata ku waye, ku daina bin son zuciyarku._

_Iyaye kuji tsoron Allah ku dinga aurar da 'ya'yanku lokacin da suka isa, domin rashin yin hakan ne yasa yan uwanmu mata suka lalace a yanzu, domin wasu matan sunada tsananin sha'awa fiye da maza kamar yadda Manzon Allah s.a.w ya gayamana._

_Manzon Allah s.a.w ya bada umarni kai tsaye a inda yace *"MATASA DUK WANDA YA SAMU IKO DA HALI NA YIN AURE THO YAYI"* kuma sanin kanmu ne cewa aure ibada ne, saboda hakane yasa kafin a kai ga zuwa neman aure akwai abubuwan da musulunci ya shar'anta maka wanda wajibine akanka kafin ka tunkari neman aure, ya zama ka kudurta a zuciyarka cewa aure hanyace da ake shiga aljanna dashi. Annabi s.a.w ya gayawa mata gameda sha'anin aure, har ma yace mijinki shine aljannarki. Tho jama'a kunga zaman aurenki bazai yiwu ba ki samu aljannah idan har bakije kin koyi yadda ake zaman aure ba, wallahi bazaki taba more ko ki ci ribar zaman aure muddin bazaki je ki koyi yadda ake zaman auren ba. Domin zaman aure baya yiwuwa da ka, wallahi jama'a baya yiwuwa da ka, saboda haka kusani cewa aure ibada ne da Allah ya shar'anta akan kowane musulmi mai ikonyi, domin ta wannan auratayyar ne ake samun rabauta mafi girmar kololuwa ta duniya kuma ake samun rabautuwa a gobe kiyama. Saboda haka iyayena mata musamman yan mata wallahi duk yadda zakiyi kiga kin samu miji nagari, tho wallahi kiyi matukar bai sabawa shari'a ba, idan Allah ya kaddara kika samu, tho wallahi ki rikeshi fiye da magnet, idan ba haka idan kika rasashi, tho da wahala ki kuma samu irinshi, domin nagartattun matasan yanzu wuya suke, kunsan dama duk abu me muhimmanci a rayuwa, tho ba a samunta da sauki. Saboda haka yanzu sai ki duba cikin samarin da kike dasu, wanene aciki kika fahimci cewa yanada dabi'u masu kyau? Wanene acikinsu kika fahimci yana da dadin zama dashi? Wanene acikinsu kika fahimci cewa zai kula da ke, kuma zai doraki akan tarbiya ta addinin musulunci? Wallahi matukar babu kwara daya acikin samarinki na yanzu, tho abinda yafi dacewa dake a yanzu shine ki rabu dasu duka, idan kikayi haka bakiyi yaudara indai dan kin fahimci cewa basuda halayya ta nagarta, tho ki rabu dasu ba ajinki bane. Idan kuwa kikayi taurin kai saboda ya tara abun duniya, tho ina me tabbatar miki sai kinyi nadamar da bazatayi amfani ba wallahi. Har yanzu akwai yanmatan da basu san yaya ake gane saurayi nagari ba, shiyasa wasu matan suke yin fushi da saurayin da ya damu akan yaya suke gudanar da ibadunta ba. Akwai wani bawan Allah wanda shi burinsa shine idan yaje zance, tho kafin su shiga babin soyayya zai fara tambayarta cewa shin kinyi sallah kuwa? Tho da zarar tace ai wallahi batayi ba, amma zuwa anjima zatayi, tho sai shi saurayin yayi fushi, tho ita kuma wawiya bazata damu ba, takamarta shine ai inada kyau, idan ma ka daina zuwa ai akwai wasu, tho wallahi masu irin wannan halin sunyi asara wallahi. Domin irin wadannan matasan ko, tho abin sone abin kwadayi ne ga mata masu hankali zallah._
=
=
_Dan uwanku na yau da kullum a musulunci da Sunnah_
°
*_✍Abdulrasheed Ibn Musa Abms_*
*_(ABU-MANAL)_*
°
°
.
Allah ta'ala yasa mudace
.
.
https://www.facebook.com/Zauren-Majalis-Sunnah-420869088334488/?referrer=whatsapp
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Post a Comment (0)