KASHE ƁARAWO YA SAƁA WA SHARI'A

*KASHE BARAWO A KASUWA YA SABAWA SHARIA*

Tambaya
Assalamu Alaikum malan barka da safiya Wai malam hukuncin kisa da ake yiwa barawo idan an kama shi, ya hallata ko kuwa bai hallatta a kashe barawo ba ? Allah ya karawa malan sani

Amsa
Wa alaikum assalam
Bai halatta ba, saboda a SHARIA hukuncin Barawo shi ne a yanke masa hannu, idan ya saci nisabi daga inda ba shi da iznin shiga.
Sannan yanke hannun Barawo yana hannun Hukuma, ita ce take da hakkin zartar Masa da haddi, hakan sai ya nuna abin da mutane suke Yi kuskure ne.

Idan Barawo ya yi kokarin yin ta'addanci aka kashe shi wajan kai dauki babu matsala in an kashe shi.
Allah ne Mafi sani

 Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
12/03/2021

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248


Post a Comment (0)