AZUMIN KWANA UKU A WATAN RAJAB


*AZUMIN KWANA UKU A WATAN RAJAB ! !*


*Tambaya*


Assalamu alaikum inayiwa malan fatan alkhairi, tambayata iyace :- Azumi uku na tsakiyar wata wanda ake kira " Ayyaamul beed " na watan Rajab
To ya hallata a muslunci?.


*Amsa*

Wa alaikum assalam,
Ya tabbata a cikin hadisin Tirmizi mai lamba ta: 761: Annabi s.a.w. ya cewa Abu-zarrin idan za ka yi azumi, to ka azumci ranar sha uku da ranar sha hudu da sha biyar daga kowanne wata, watan Rajab Daya ne dağa cikin watannin musulunci za'a iya azumin da ya tabbata a ragowar watanni a cikinsa, sai dai kawai watan bai kebanta da Wata falala ba.

Allah ne mafi sani. 

21\4\2016.

*Amsawa:* Dr. Jamilu Zarewa.
*Gabatarwa:* Abu- Unaisa.

👉🏾 Darussunnah Foundation, 07035888158.
Post a Comment (0)