NEMAN AURE A SAUDIYYA


Tsokaci:

Neman aure a Saudi Arebia.

 Ina sauraren Dr. Mansur Yelwa, cikin wani lacca yake cewa: Su a al'adar Saudi Arabia idan kana son d'iya mace, kai baka taba ganin ta ba, kadai San gidan su wane akwai d'iya mace tana zuwa makaranta, ko da yaushe kuma a rufe take idan zata fita, fuska a rufe ko ina ruf. Idan tana tafiya zadai kaga wani abu yana motsi sabida kyakkyawan shiga (ba'a gane ta, sunan ta de mace) BMO (black moving object), to, idan kana son Kasan yaya take, ya ya karan hancinta yake da kwarmin idon ta, zaka zo ka tura wata gwaggonka ko kanwarka ko yayarka ne taje gidan su ganin ta idan ta gano se tazo ta gaya maka, idan aka ce an baka izini se ka zo gidan ganin ta, to, nan fa zata taho ne da mahaifin ta yana gaba tana baya ko wani babban yayanta ya zauna, ace ta kawo shayi a Kofi ta ajiye ta koma ta zauna, to ko anan zaka ga tafiyar ta, to irin wannan lokacin idan ka yi sa'a zata daga niqabi, ba mamaki shine farkon lokacin da ta taba daga niqabi gaban wani Wanda ba muharramin ta ba, wata ma baza ta iya dagawan ba, to nan baban nema zai maka bayani may be yace kada ka ji ta yi shiru, tana magana ba kurma bace...

Tanbihi:
Wasun mu anan, Wata kafin ayi auren duk jikin ka da nata sun gogi juna? sabida rashin tsoron Allah, da son zuciya? Kuma de se ace ana son albarka? Ko ba haka ba, ko ba zaka aura ba, zaka gane ta araha gata nan. Wallahi mata kuna da kima da daraja, bai kamata ace kowa zai ganki da ko wani irin kwalliya se Wanda shari'a ta yarda da shi. Ya kamata mu gyara musan kimar mu da mutuncin mu duk lokacin da mace take rufe tafi daraja.

Note
Malam ya dan yi tsokaci kadan akan maganganun malaman fighun kan neman auren mu dama nasun mai son jin bayanai dama Wanda ba wannan ba se ya nemi lacca din Mai taken "Illolin wayar hannu a cikin Al'umma"

 Allah Ta'ala yasa mu gama lfya.

✍️ Salma Nakumbo


_WhatsApp Group_
*_+2348038783913_*

https://www.facebook.com/102625061694017/posts/126034532686403/?app=fbl
Post a Comment (0)