BIDI'O'IN WATAN RAJAB 01


*_BIDI’O’IN WATAN RAJAB_*

Darasi na farko-(1)

Dukkan yabo da godiya da kirari da jinjina sun tabbata ga Allah madaukakin sarki,wanda ya cancanci a bauta masa shi kadai,baya da wani abokin tarayya acikin bautarsa,kamar yadda baya da abokin tarayya acikin aiykansa da sunaynesa da siffofinsa.Tsira da amincin Allah su kara tabbata a bisa Bawansa kuma Manzon Annabi Muhammad ﷺ , cika makin Annabawa kuma shugaban dukkan Manzanni,salatin Allah ya kara tabbata agareshi da iyalin gidansa masu tsarki da dukkan sababbansa yardaddun Allah da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa.

*WATAN RAJAB*
Watan Rajan dayane daga cikin watanni guda hudu masu alfarma acikin watannin shekara,kamar yadda Allah Madaukakin sarki yake fada:-
(ﺇِﻥَّ ﻋِﺪَّﺓَ ﺍﻟﺸُّﻬُﻮﺭِ ﻋِﻨْﺪَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﺛْﻨَﺎ ﻋَﺸَﺮَ ﺷَﻬْﺮﺍً ﻓِﻲ ﻛِﺘَﺎﺏِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻳَﻮْﻡَ ﺧَﻠَﻖَ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْﺽَ ﻣِﻨْﻬَﺎ ﺃَﺭْﺑَﻌَﺔٌ ﺣُﺮُﻡٌ ﺫَﻟِﻚَ ﺍﻟﺪِّﻳﻦُ ﺍﻟْﻘَﻴِّﻢُ ﻓَﻼ ﺗَﻈْﻠِﻤُﻮﺍ ﻓِﻴﻬِﻦَّ ﺃَﻧْﻔُﺴَﻜُﻢْ ﻭَﻗَﺎﺗِﻠُﻮﺍ ﺍﻟْﻤُﺸْﺮِﻛِﻴﻦَ ﻛَﺎﻓَّﺔً ﻛَﻤَﺎ ﻳُﻘَﺎﺗِﻠُﻮﻧَﻜُﻢْ ﻛَﺎﻓَّﺔً ﻭَﺍﻋْﻠَﻤُﻮﺍ ﺃَﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻣَﻊَ ﺍﻟْﻤُﺘَّﻘِﻴﻦَ ) ( ﺍﻟﺘﻮﺑﺔ :36 )
Ma'ana:
*(Lallai ne ƙidãyayyun watanni a wurin Allah watã gõma shã biyu ne a cikin Littãfin Allah, a Rãnar da Ya halicci sammai da ƙasa daga cikinsu akwai huɗu mãsu alfarma.Wannan ne addini madaidaici. Sabõda haka kada ku zãlunci kanku a cikinsu. Kuma ku yãƙi mushirikai gabã ɗaya, kamar yadda suke yãƙar ku gabã ɗaya. Kuma ku sani cẽwa lallai ne Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa)*.

Watanni masu alfarma sune:-
*i-Almuharram*
*ii-Rajab*
*iii-Zul-iqdah
*iv-Zul-Hijjah
Kamar yadda Annabi ﷺ , ya tabbatar a Hadisin Sayyadin Abubakar Saddiq R.A,Manzon Allah ﷺ ,yana cewe:
*(Lallai zamani ya kusanta kamar yadda yake a ranar da Allah ya halicci Sammai da Kassai, shekara wata goma sha biyune,acikin su akwai watanni guda hudu masu alfarma,guda ukku masu biyene da juna sune,zulqidah zulhijjah da Almuharram,da kuma watan RAJAB wanda yake tsakanin Jimada da Sha'aban)*.
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( 4662 ‏) ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏( 1679 ).

*_MIYASA AKE KIRANSU DA WATANNI MASU ALFARMA??_*
i-An kiraye sune da watanni masu alfarma saboda haramta yaki acikinsu,sai dai idan abokan gaba sun kawo maku hari,to anan babu laifi ku kare kanku.
ii-Saboda da hanin yaki acikin watan Rajab yafi tsanani acikinsa fiye da sauaran dukkan watanne masu alfarma.

*MIYASA AKE KIRAN WATAN RAJAB DA RAJAB??*
Ana kiran watan Rajabne da RAJAB saboda labarawa sun kasance suna giramamasa tun a zamanin Jahiliya.
@ﻟﻄﺎﺋﻒ ﺍﻟﻤﻌﺎﺭﻑ / 225

*GADA CIKIN BIDI'OIN WATAN RAJAB*
_1-BIDI'A TA FARKO_
*"Yin Adduar shiga watan Rajab,da wata addua ta musamman"*

An ruwaito wata addua wadda ta shahara abakunann mutane wadda ake karantawa a farkon watan Rajab,ana kiranta adduar shiga watan Rajab,Adduar itace;-
*[ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺑﺎﺭﻙ ﻟﻨﺎ ﻓﻲ ﺭﺟﺐ ﻭﺷﻌﺒﺎﻥ ﻭﺑﻠﻐﻨﺎ ﺭﻣﻀﺎﻥ]*. 
An ruwaito cewa Manzon Allah ﷺ ya kasance idan watan Rajab ya shigo yana karanta wanna addua:
( ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺑﺎﺭﻙ ﻟﻨﺎ ﻓﻲ ﺭﺟﺐ ﻭﺷﻌﺒﺎﻥ ﻭﺑﻠﻐﻨﺎ ﺭﻣﻀﺎﻥ ‏) .
@ ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ 1/259 ﻭﺍﻟﺒﺰﺍﺭ ‏( 616 ﺯﻭﺍﺋﺪ ‏) ﻭﺍﻟﻄﺒﺮﺍﻧﻲ ﻓﻲ ﺍﻷﻭﺳﻂ ‏( 3939 ‏) ﻭﺍﻟﺒﻴﻬﻘﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﺸﻌﺐ ‏( 3815 )
Sai dai Manyan Malaman Hadisi sunce Hadisin Bai ingantaba,saboda riwayar wanine wanda ake kira da
" ﺯﺍﺋﺪﺓ ﺑﻦ ﺃﺑﻲ ﺍﻟﺮﻗﺎﺩ ﻋﻦ ﺯﻳﺎﺩ ﺍﻟﻨﻤﻴﺮﻱ ".
Imam Bukhari yana cewa:
" ﻣﻨﻜﺮ ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ "
"Wato hadisansa Munkaraine".
@ﺷﻌﺐ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ 3/375
Kuma Alhafiz ibn Rajab da Hafiz Ibn Hijir Allah yayi masu Rahama sun raunanshi.
@ﻟﻄﺎﺋﻒ ﺍﻟﻤﻌﺎﺭﻑ /234 ).

A takaice wannan hadisi bai tabbata ba daga Annabi ﷺ ba yana karanta wannan adduar ba a farkon watan rajab ba,kuma karanta wannan adduar bidiace.
Allah ne mafi sani.


Mu hadu a Darasi na biyu insha Allah.
Post a Comment (0)