GUZURIN ME AZUMI DON SHIGA WATAN RAMADAN


*_GUZIRIN MAI AZUMI DAN SHIGA WATAN RAMADANA_*

*Ma’anar Azumi*
Minene Azumi??


Amsa;
Azumi a yaren Larabci yana nufin;
*kamewa ko Kamewa da barin wani abu*

*i-Ma’anar Azumi a Shari’a;

ﺍﻟﺤﺎﻓﻆ ﺍﺑﻦ ﺣﺠﺮ ـ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ
Yana cewa:
*Azumi yana nufin kamewa kebantacciya,daga wadansu abubuwa sanannu,awani zamanin sananne,da wani sharadi sananne”*
@ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻖ ﻋﻠﻲ ﻓﺘﺢ ﺍﻟﺒﺎﺭﻱ.

Fa’ida;
Wato yana nufin
*“Kamewa daga ci da sha da kusantar iyali da sabon Allah,tun daga fitowar alfijir har yazuwa faduwar rana”*

ii-Ma’anar Azumi a Shari’a
ﺍﻟﻌﻼﻣﺔ ﺍﻟﻌﺜﻴﻤﻴﻦ ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ;
Yana cewa:
*Azumi shine bautama Allah shi kadai ta hanyar kamewa daga ci da sha,da nisantar dukkan abinda yake karya azumi tun daga fitowar alfijir na gaskiya har ya zuwa faduwar rana”*
@ﺍﻟﺸﺮﺡ ﺍﻟﻤﻤﺘﻊ.

iii-Ma’anar Azumi a Shari’aShine;
*Kamewa daga Sha’awar ciki waton cin abinci,da kamewa daga Sha’awar al’aura,wato barin jima’i da dukkan abinda yake motsa sha’awa,acikin yini baki daya,da niyyar bautar Allah*.
@ﺍﻟﺸﺮﺡ ﺍﻟﻜﺒﻴﺮ ﻟﻠﺸﻴﺦ ﺍﻟﺪﺭﺩﻳﺮ.
iv-Ma’anar Azumi a Shari’a
*Shi ne bautawa Allah ta hanyar kamewa daga cin abinci da abin sha da jima’i,tun daga hudowar alfijir har zuwa faduwar rana*

v-Ma’anar Azumi a Shari’a
*Neman kusanci zuwa ga Allah Ta’ala ta hanyar kamewa daga ci da sha da jima’a da sabon Allah,tun daga fitowar alfijir na biyu har zuwa faduwar rana da neman bautar Allah*.


Allah ne mafi sani

Zamu kwana a nan sai a Darasi na gaba insha Allah.
Post a Comment (0)