TUMATIR


🌸 *JIKIN DAN ADAM* 0️⃣6️⃣0️⃣🌸

🍅 *_TUMATIR_*🍎 1️⃣

_Tumatir dai mahadi ne sananne ga mutane masu dama a mabambantan abinci, kodai a dafa shi, ko a soya, ko ma a ci danye, yana da kaloli daban-daban, amma wanda aka fi sani shi ne ja, sai dai akwai ruwan lemo, rawaya har ma da ruwan malmo, gwargwadon qasashen da suke amfani da shi, a taqaice dai, wasu fa'idoji ne ake samu a cikin Tumatir? Ya za mu yi aiki da shi don samun fa'idojin da suke cikinsa? Ko yakan yi maganin wasu cututtuka? Shi kuma me da me ya qunsa? Ko cinsa da yawa zai iya wahalarwa? Wadannan da wasunsu muke so mu tattauna a ciki in sha Allahu ta'ala_. 

_Tumatir daya ne daga cikin jinsin yalo, amma ana daukarsa a matsayin ganyayyaki sabo da Antacid, ana qiyasta cewa Tumatir yakai kala 600 a duniya, Tumatir yana da amfani a jiki gwargwadon yadda mutum zai ji ya kuma kiyaye, yakan taimaka wajen kawar da qwayoyin cutar da suke cutar da jikin dan adam, yakan dawo da nashadin qoda yadda zai yi aiki kamar yadda ya dace sabo da samun Vitamin A, C mai dama a cikinsa, yakan yi aiki a matsayin sinadarin wanke ciki da hanji, yakan kawar da wahalar da ciki yake fama da ita wajen markade abinci, sananne ne cewa Tumatir ya qunshi Iron, wanda yake fama da fatarar jini zai iya shan juice din Tumatir ko ya ci danyensa_. 

_Akan yi aiki da Tumatir don magance gurbataccen ruwan sinadarin dake jiki, haka wahalar yin numfashi da wani lokaci yakan yi wahala ga dan adam, yakan yi amfani ga masu ciwon sukari, sabo da ba shi da Carbohydrates mai yawa a cikinsa, haka ciwon gabobi, Tumatir kan magance shi ta wajen zuba masa mai a dan ba shi tsoro a wuta sai a shafa a inda yake cutarwan, kasancewar Tumatir yana dauke da kashi 95% na ruwa yana iya daidaita qibar mutum, ga shi bai da Calories mai dama. Tumatir yakan samar da Vitamin C mai kyau, Provitamin A ko Carotene, Vitamin A wanda yake Antioxidant ya taimaka wa garkuwar jiki, wani binciken ya nuna cewa yakan yi maganin wasu nau'o'i na Cancer ciki har da na mabubbugar maniyi, da na huhu, sabo da yana dauke da sinadarin Lycopene wanda shi ne yake sanyawa launin Tumatirin ya zama ja,_

_Tumatir yana dauke kuma da Minerals wadan da ake dan shan wahalar samu, irin su Potassium da yake inganta qoda, da Phosphor, Calcium da Magnesium._

Muhadu a rubutu na gaba in shaa Allah

📒 *Abu manar Alqasim*
✍🏻 *Ibnmangaa*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Post a Comment (0)