HUKUNCIN ASKE GEMU!!
TANBAYA
Assalamu alaikum.
Malam mene ne hukuncin tsayar da gemu? shin wajibi ne ko mustahabbi? Sannan aske shi haramun ne ko makaruhi ne? Watau yinsa banza barinsa banza.
.
.
AMSA
Wa'alaykumussalam, To dan'uwa Annabi (S.A.W) yana cewa: "Ku sabawa mushrikai, ku cika gemu, ku rage gashin baki". Kamar yadda ya zo a hadisin Bukhari mai lamba ta: 5553 da kuma Muslim a lamba ta: 259.
Wannan yasa da yawa daga cikin malamai suka tafi akan wajabcin tsayar da gemu da kuma haramcin aske shi, har ma wasu malaman kamar Ibnu Hazm sun hakaito ijma'in malamai akan haka, kamar yadda ya zo a littafinsa na Maratibul Ijma'i shafi na: 157.
.
.
Malamai suna cewa har abin da aka rawaito daga wasu sahabbai kamar Ibnu Umar cewa suna rage gemu idan ya kai wani geji, to suna yi ne lokacin hajji saboda suna ganin hakan na daga cikin rage kazantar da Alhaji ya kan yi bayan ya gama aikin hajjinsa.
Sannan gemu na daga cikin abubuwan da ke karawa namiji kwarjini da kyau, shi ya sa za ka ga wanda yake aske shi yana kama da tsohuwar da kyanta ya disashe, kamar yadda Sa'adi ya fadi a Bahjatu kulubul Abrar shafi na: 50.
Sai dai malamai suna cewa mutum yana garin da za a iya kashe shi idan ya bar gemunsa, to zai iya askewa saboda lalura, sai dai ya wajaba kowacce lalura kar ta wuce gwargwadonta.
Don neman karin bayani duba littafin: Wujubu I'ifa'ul liha
Allah ne mafi sani.
18/10/2014
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa
ZaKu iya Bibiyar Mu a
WhatsApp
+2348137195108
Ko
Telegram https://t.me/tafarkintsira