HUKUNCIN SHAN MAGANIN ƘARA ƘIBA


*HUKUNCIN SHAN MAGANIN QARA QIBA?*

https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN

*TAMBAYA*❓

Shin ko ya halatta Mutum yasha maganin kara kiba idan yakasance ramammene shi??

*AMSA*👇

Dangane da hukuncin shan magani domin neman ƙara ƙiba ajiki kokuma dan saboda wani sashe na jikin Mutum yaƙara girma kamar misali Mace tasha magani danufin Nonuwanta kokuma Ɗuwawunta suƙara girma, bayanin da Malamai sukayi akan haka shine, akwai wanda yahalatta agareshi yasha maganin ƙara ƙiba, akwai kuma wanda haramunne agareshi yasha wannan magani, wato ya dangantane da niyya ko sababin da yasa za'ayi amfani da wannan magani,
:
Idan yakasance Mutum yana da wani aibu ko naƙasa ajikinsa wanda yawuce irin wanda akasaba ganin Mutane dashi abisa al'ada, kamar misalin Mutumin da yayi Accident wani sashe na jikinsa ya lalace ko wanda haƙoransa suka fito waje dayawa zaƙo-zaƙo, ko yakasance Mutum arame yake sosai irin ramewar da tawuce wadda akasaba gani a al'ada, kuma koda yanacin abinci maigina jiki haka yake baya ƙaruwa to ayanayi irin wannan Malamai sukace idan masana kiwon lafiya (Likitoci) suka bashi shawarar cewa yasha maganin ƙara ƙiba to ya halatta yasha, kokuma ayiwa Mutum aiki dan akawar da wannan aibu ko naƙasar dake tare dashi, domin anyimasa hakane danufin akawar dawannan naƙasa dake tare dashine kawai danhaka babu laifi,
:
Amma idan yakasance babu wata naƙasa ajikin Mutum irin naƙasar da tawuce wadda akasaba gani abisa al'ada, Saidai kawai Mutum zaisha maganin ƙara ƙibane danufin yaƙara masa kyau, kokuma Mace tasha magani danufin Ɗuwawunta suƙara girma ko danufin Nonuwanta suƙara girma idan yakasance ƙananane, kokuma arage musu girma idan sun kasance Nonuwanta manyane sosai, domin taƙara kyau dan tariƙa burge Mutane:, kokuma saboda kasancewar Mutum bashi da jiki sosai acikin abokansa sai yakeso yasha magani danufin jikinsa yakoma irin nasu, da dukkan wani wanda zeyi amfani dawani magani danufin yaƙara kyau bawai wata larura bace mai tsanani tasa yabuƙatu da dole sai yayi hakanba, to dukkan waɗannan abubuwa da makamantansu haramunne aikatasu, domin yashiga ƙarƙashin hukuncin masu jirkita halittar Aʟʟαн( ﷻ ) domin dama Shaiɗan yafaɗa cewa sai ya umarci Mutane suna jirkita halittar Aʟʟαн( ﷻ ) kamar yadda Aʟʟαн( ﷻ ) Yafaɗa acikin wannan aya:
:
" ﻭﻵﻣﺮﻧﻬﻢ ﻓﻠﻴﻐﻴﺮﻥ ﺧﻠﻖ ﺍﻟﻠﻪ "
Sai na umarcesu da suriƙa jirkita halittar Aʟʟαн( ﷻ )
:
Danhaka abune mai matukar hadari haka kawai Mutum yace zaisha maganin kara kiba danufin yakara kyau, yakamata asani cewa, dukfa yadda Mutum yakaiga rena kansa to ahakan shi abin sha'awane awajen wasu Mutanen, hakanan kuma duk yadda Mutum yakaiga jirkita halittarsa danufin yakara kyau, to ko rabin-rabin kyaun wani bazai taba kaiwa ba, danhaka garama Mutum ya hakura da yadda Mahaliccinsa ya halicceshi sai yazauna lafi lafiya,
:
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαппαп ʟıттαғı καмαя нακα:
" ﻓﺘﺎﻭﻯ ﺇﺳﻼﻣﻴﺔ " ‏( 4/412

→AMSAWA←
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF* ‏
Post a Comment (0)