HUKUNCIN TSALLAKE TA GABAN ME SALLAH


*HUKUNCIN TSALLAKE TA GABAN MAI SALLAH* 

https://chat.whatsapp.com/KeXayNmsBie671pMAKT9xN

 *TAMBAYA* ❓

Assalamu alaikum. Fatan Malam yana cikin koshin lafiya Allah yasa haka ameen, Allah ya biya da gidan aljanna bisa qoqarin da ake damu. Tambaya ta Malam menene hukuncin tsallake gaban mai sallah? Kuma naji ance wai idan wani ya wuce ma ta gaban sallar ka ta 6aci? Allah ya bada ikon amsawa.


 *AMSA* 👇


Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Hadisi ne Ingantacce. Manzon Allah saw Yace. DA WANDA ZAI WUCE TA GABAN MAI SALLAH YA SAN ABINDA ZA'A RUBUTA MASA NA ZUNUBI. DA YA ZAUNA HAR TSAWON ARBA'IN.
 Malamai suka ce gwanda ya Tsaya ya Jira Wannan mai sallar har ya gama, ko da zai Kai tsawon Shekara 40, Wasu Suka ce wata 40, Wasu suka ce Sati 40 Wasu kuma suka ce Kwana 40.
 Ko yaya ne ma dai. Manzon Allah saw yana son ya Nunawa Al'ummarsa Girman Zununin Wucewa ta gaban Mutum a Lokacin da yake yin sallah. Harma Wasu Malaman sun Ambaci Wucewa ta Gaban Mai Sallah a Cikin Manya-Manayan Zunibai da dan Adam zai Aikata a Rayuwar Sa.

  Magana ta Biyu kuma shine. Idan mace ko Jaki Ko Bakin Kare ya Wuce ta gaban Mai sallah ba tare da Sutura a gabansa ba. Manzon Allah saw Yace Sallar sa ta Lalace. Har sai ya sake yin wata Sabuwa.

 Allah shine Masani.

Zaku iya samu wannan group na Facebook ta wannan hanyar👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Join us on Facebook🖕
Post a Comment (0)